Innalillahi: Ɗaruruwan Mutane Sun Raunata A Wani Mummunan Hari
Asibitoci Sun Cika Da Ɗaruruwan Waɗanda Suka Samu Raunuka A Goma.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce asibitoci sun cika maƙil da 'daruruwan majinyata da suka samu raunuka a gabashin Goma, inda ƴan tawayen M23 da Ruwanda ke goyon baya suke yunƙurin ƙwace birnin daga sojojin Congo.
Akwai gawarwaki da dama kan tituna ya yinda ake ci gaba da fafata yaƙi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu rahotannin yadda mayaƙan suka aikata fyade.
Dr Adelheid Marschang babbar jami'ar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce WHO ta damu musamman da lafiya da tsaron mata da ƴan mata da masu juna biyu wadanda ke cikin hatsari, dama akwai yawaitar mutuwar masu juna biyu ya yin haihuwa tun kafin ɓallewar rikicin.
Hukumar Lafiya ta Duniya na aiki tare da hukumomi da abokan hulda don neman mafita.

Comments
Post a Comment