Turkashi! An Maka El-Rufai Kotu Kan Zargin lmundahana

ICPC Ta Maka El-Rufai A Kotu Kan Zargin Almundahana.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon kwamishinansa, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi.

Jami'in shari'a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka El-Rufai da Bashir Saidu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa.

A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohon gwamnan ta almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.