Turkashi! Shugaban Gwamnatin Ostiriliya Zai Yi Murabus Bisa Wasu Dalilai
Shugaban gwamnatin Ostiriya Karl Nehammer Zai Yi Murabus.
Shugaban gwamnatin Ostiriya mai ra'ayin mazan jiya, Karl Nehammer, ya ce zai yi murabus nan da kwanaki masu zuwa bayan da tattaunawar kawance tsakanin jam'iyyarsa ta People's Party da Social Democrat ta wargaje.
Nehammer ya ce sun kasa cimma yarjejeniya kan wasu muhimman batutuwa.
Ƙungiyoyin siyasa guda uku sun yi ta ƙoƙarin ganin sun cimma matsaya bayan da jam'iyyar Fredom party, mai kusanci da Rasha ta lashe zaɓe a watan Satumba.
Zaɓin da ya rage shi ne ko a bai wa jam'iyyar Freedom Party wadda ta lashe zaɓe damar kafa gwamnati ko kuma a sake wani sabon zaɓe idan hakan ya faskara

Comments
Post a Comment