Wata Sabuwa: Magoya Bayan Peter Obi Sunyi Allah Wadai Da Barazanan Rayuwarsa.
Magoya Bayan Peter Obi Sun Yi Allah-wadai Da Barazana Ga Rayuwarsa.
Magoya bayan tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya, Peter Obi, wato Obidient sun yi Allah-wadai da barazanar da ya ce ana yi wa rayuwarsa.
A wata sanarwa da Yunusa Tanko ya fitar a madadinsu, ya ce suna takaici kan jawabin Felix Morka wanda sakataren watsa labaran APC ne na ƙasa ya yi a tashar Arise.
Sanarwar ta ce, "maganarsa cewa Peter Obi ya tsallake iyaka barazana ce ga rayuwarsa, kuma barazana ce ga zaman lafiyar Najeriya.
"Wannan na nuna yadda Najeriya take ƙara faɗawa cikin mulkin kama-karya a wannan gwamnatin, domin a ce irin wannan jawabin na fitowa daga bakin kakakin jam'iyya mai mulki bai da ce ba, kuma tamkar kira ne ga tayar da zaune tsaye.
Sanarwar ta kuma yi tambayar "wane ne ya shata layin, kuma wane layin ne Obi ya tsallaka?" sannan suka yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa.

Comments
Post a Comment