Yanzu-Ynazu: Donald Trump Na Shirin Ganawa Da Putin
Ina Shirye-Shiryen Ganawa Da Putin-Trump.
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ana shirya yadda zai gana da shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin.
Sai dai Mista Trump bai bayyana lokacin da za a yi ganawar ba
Yayin da yake jawabi a jihar Florida, shugaban Amurkan mai jiran gado ya ce "Putin na so mu gana, kuma muna shirya yin hakan."
Kamfanin dillancin labarai na Rasha, Tass ya ambato kakakin gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov na cewa, har yanzu Amurka ba ta gabatar da buƙatar ganawar a hukumance ba.
Trump ya alƙwarta tattaunawa da Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da zarar an rantsar da shi ranar 20 ga watan Janairu, sannan ya bayyana shakku kan tallafin soji da Amurka ke bai wa Ukraine.
"Putin na son ganawarmu, kuma ya bayyana ƙarara cewa ya kamata mu kawo ƙarshen wanann yaƙi, wanda ke zubar da jinin al'umma,'' in ji shi.
Mista Trump ya naɗa Keith Kellogg, tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, kuma tsohon babban janar a rundunar sojin ƙasar a matsayin Jakadan Amurka na musamman kan Rasha da Ukraine.
Tuni dai Kellogg ya fara zayyana wasu tsare-tsaren da Amurka za ta bi don kawo ƙarshen yaƙin na Ukraine, ciki har da batun cewa Ukraine za ta samu ƙarin tallafin soji ne kawai idan ta amince da da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.

Comments
Post a Comment