Yanzu-Ynazu: Girgizar ƙasa Tayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Sama Da 75 A China

Aƙalla Mutum 95 Sun  Rasu A Girgizar ƙasa A China.

Bayanan hoto,Aƙalla gidaje 1,000 ne suka ruguje a girgizar ƙasar sannan mutum 95 suka rasu

Wata mummunar girgizar ƙasa ta afku a kusa da iyakar Tibet da Nepal.

Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da 130 sun jikkata a girgizar, wadda ta afku a ranar Talata.

Girgizar ta kuma ƙetara zuwa yankin Nepal da ke ƙasar Indiya, wanda ke maƙwabtaka da Tibet na ƙasar China.

Girgizar ƙasar ta lalata gine-gine a birnin Shigatse na Tibet, lamarin da ya sa jama'a su riƙa kwararowa kan tituna domin tsira. 

 Tuni sojojin ƙasar suka fara aikin ceto, inda suka aika jirage marasa matuƙa zuwa wani yanki mai nisa a kusa da tsaunin Everest

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.