Yanzu-Ynazu: An Naɗa Gabduje Shugaban Kwamitin Gudanarwa Na FAAN

Tinubu Ya Naɗa Ganduje Shugaban kwamitin Gudanarwa Na FAAN.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban jam'iyar APC, Abdullahi Umar Ganuje a matsayin shugaban hukumar gudanarwar sufurin jiragen sama, FAAN.

Tinubu ya kuma naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna a matsayin shugaban hukumar bankin bayar da rancen sayen gida, wato Morgage bank.

Haka kuma shugaban ya naɗa sakataren jam'iyar APC na ƙasa, Sanata Bashiru Ajibola a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NSDC.

Mai magana ba shugaban ƙsar shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya sanar da naɗe-naɗen a cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Juma'a.

"Shugaban Tinubu ya naɗa shugabannin hukumar gudanarwa 42 na ma'aikatun gwamnatin tarayya da sakataren hukumar gudanarwa na gidajen yari da hukumar shigi da fici da kuma ta hukumar tsaro da kai dauki ta Civil Defence," Cewar sanarwar.

Sannan shugaban ya naɗa kanen ministan ayyuka, Augustine Chukwu Umahi, a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.