Yanzu-Ynazu: Rikici Ya Barke Tsakanin Boko Haram Da Dogo Gide
Dogo Gide Ya Gwabza Fada da Mayakan Boko Haram.
An sheke 'Yan Ta'adda Masu Yawa A Yau Alhamis, Janairu 23, 2025 Da Yamma. Tantirin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya tsallake rijiya da baya bayan mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Sadiku sun yi masa kwanton ɓauna.
Dogo Gide ya bayyana cewa ya yi nasara kan ƴan ta'addan inda ya kashe aƙalla guda 20 daga cikinsu tare da ƙwato makamai Dangantaka ɗai ta yi tsami ne tsakanin Dogo Gide da ƴan Boko Haram tun bayan da aka kashe masa ɗan uwansa a shekarar 2023.
Jihar Zamfara - Hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya gwabza faɗa da mayaƙan Boko Haram.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Comments
Post a Comment