Yanzu-Ynazu: Tinubu Yayi Shirin Yima 'Yan Nigeria Aiki.
Gwamnatin Tinubu Ta Samo Rancen Sama Da N1bn Don Tsame Najeriya Daga Duhu.
Bankin AfDB zai ba da Dala miliyan 200 domin aiwatar da shirin wutar lantarki na Najeriya, wanda zai baiwa mutane 500,000 hasken lantarki.
Wannan ya na daga cikin Dala biliyan 1.1 da Najeriya ta karba domin aiwatar da ayyukan samar wa 'yan kasa hasken wutar lantarki zuwa 2026 Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na ganin wannan makudan kudi da ya ke karbo wa za su taimaka wajen raba Najeriya da duhu.
Abuja - Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar da samun bashin Dala biliyan 1.1 daga Bankin Raya Afrika (AfDB) domin gudanar da aikin samar da hasken wutar lantarki a kasar.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana hakan, ya ce ana sa ran samar da hasken wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen shekarar 2026.

Comments
Post a Comment