Yanzu_Yanzu: Apple zai biya Tarar Dala Miliyan 95 kan Manhajarsa Ta Siri.
Apple zai biya Tarar Dala Miliyan 95 kan Manhajarsa Ta Siri.
Kamfanin Apple ya amince ya biya tarar dala miliyan 95 a ƙarar da aka shigar da shi kotun Amurka kan zargin manhajarsa ta Siri na sauraron tattaunawar sirri ta masu amfani da ita.
Masu amfani da wayoyin Apple da kamfutarsu ta hannu wato Ipad da sauraron kamfutoci na zargin Siri da naɗar muryarsu a wasu lokutan, ko da ba su kunna ta ba.
Sannan kuma suna zargin Apple da sace bayanan sirrinsu domin bai wa wasu kamfanonin. Sai dai Apple ya ce bai aikata wani laifi ba. Za dai a raba kudin ne tsakanin wadanda suka shigar da ƙarar.

Comments
Post a Comment