Yanzu_Yanzu: An Harbe Ƴan Israela A Gaɓar Yamma.
An Harbe Ƴan Isra'ila Uku A Gaɓar Yamma.
An harbe wasu ƴan Isra'ila guda uku a wani hari da aka kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Mata biyu waɗanda suka kai shekara 60 suna cikin waɗanda aka harbe.
Rundunar tsaron Isra'ila ta ce wasu ƴanbindiga ne suka buɗe wuta kan motocin fararen hula guda uku a lokacin da suke wucewa ta wani ƙauyen yankin mutanen Falasɗinu mai suna Al-Funduq wanda ke kusa da garin Yahudawa na Kedumim.
Tuni jami'an tsaron Isra'ila suka kafa shingayen bincike a yankin da zimmar kama waɗanda suka kai harin.

Comments
Post a Comment