Yanzu_Yanzu: Matsayar Nasiru El Rufa'i Akan Sauya Sheka

 

APC: El Rufa’i Ya Bayyana Matsayar Sa Kan Jita Jitar Sauya Sheka.

, Nasir El-Rufa’i, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa ya bar jam’iyyarsa ta APC El Rufa'i, wanda tsohon Ministan Abuja ne ya ce labarin kanzon kurege ne, kuma ba zai lamunci irin wannan ba Ya ce zuwa yanzu ya gano wadanda ke jagorantar yada labarin bogin, kuma tuni ya ba lauyoyinsa umarni kan batun 

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Rahotannin sun fara yaduwa ne bayan wasu kalaman El-Rufa’i da ake ganin suna sukar zargin wariyar kabilanci a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. 

sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufa’i ya wanke kansa daga zargin komawa PDP, inda bayyana rahoton a matsayin karya tsagwaron da ba shi da tushe. 

El Rufa'i ya gano masu yada komawarsa PDP A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya gano wadanda ke jagorantar yada wannan karya, inda ya zarge su da yunkurin bata sunansa tare da haddasa rudani.

 Ya kuma gargadi masu yada wannan labari cewa ba zai yarda da irin wannan cin zarafi ba, yana mai kiran su da sunan masu yada farfaganda mara gaskiya da son rijiya siyasarsa.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.