Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Kasa(Nigeria) Ta Bukaci A Jinkirta Amfani Da kwamfi:uta A Jarabawar WAEC Da NECO

Majalisar wakilan Najeriya bukaci da a ɗage afara  amfani da kwamfuta a jarrabawar WAEC Da NECO 


Majalisar wakilan Najeriya tayi  yin kurin kira ga gwamnatin ƙasar (Nigeria) ta dakatar da shirye-shiryen da hukumar tsara jarrabawar gama  sakadire ta WAEC da NECO ke yi na fara  amfani da kwamfuta a jarrabawar shekarar dubu biiyu da ashirin da shida (2026), inda ta yi gargaɗin za a iya samun dalibai da dama da za su yi rashin nasara.

Hakan ya samo asali ne akan wani kuduri da ɗan majalisa Kelechi Nworgu ya gabatar, inda ya buƙaci majalisar ta shiga tsakani kan abin da ya ce zai iya zama barazana ga fannin ilimin Nigeria baki daya 

Yakara da cewa duk da dai ana amfani da kwamfuta a jarrabawar JAMB, da POST UTME, halin da akasarin makarantun sakandire ke ciki a faɗin kasar ya sa ya ke ganin sauyawa zuwa kwamfuta a jarrabawar Daubu biiyu da ashirin da shida (2026) ya yi wuri.


A ra'ayina wannan bai kamanta a maida amfani da kwamfita Jarabawar WAEC Da NECO ba. Saboda da hakan zai haifar da yawan faduwan dalibai a Jarabawa.

Dan majalisar ya bukaci ma'aikatar ilimi da hukumar shirya jarrabawar ta WAEC su ɗage fara amfani da kwamfuta na tsawon shekaru uku, kafin nan an ɗauki matakan da su ka dace tare da samar da kayayyakin aiki.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.