Da Dumu-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Mutanen 11



A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga sun sake kai farmaki inda suka yi garkuwa da mutane 11 a wani sabon hari da suka kai wa al’ummar Isapa da ke karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara, lamarin da ya haifar da tashin hankali a yankin.


 Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata, makonni biyu kacal bayan an kai wani hari makamancin wannan a karamar hukumar, inda aka kwashe masu ibada 38 a wata Coci da ke Eruku.


 A cewar majiyoyin yankin, maharan wadanda yawansu ya haura 20, sun sauka a Isapa ne da tsakar rana, inda suka iso da garken shanu tare da harbin makamansu ba gaira ba dalili.


 Sakamakon harbin da aka yi, wata tsohuwa ta samu rauni sakamakon wani harsashi da ya bata.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.