Inalillahi! Boko Haram Sun Kai Ma Sojojin Nigeria Mummunn Farmaki A Jihar Borno
'Yan ta'addar Boko Haram sun kai wa tawagar sojojin Najeriya kwanton bauna a Borno inda suka yi awon gaba da wani Birgediya-Janar.
Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da harin da kuma matsayin jami’in da aka sace. Da yammacin jiya Juma'a ne wasu da ake zargin mayakan kungiyar IS ne daga yankin yammacin Afirka (ISWAP) suka yi wa ayarin motocin sojoji kwantan bauna a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kashe sojoji da dama da kuma jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF).
Maharan dai na dauke da makamai da tsari sosai, inda suka aiwatar da wani farmakin hadin gwiwa a kan ayarin motocin wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama da kuma firgici a yankin. A wani lamari mai ban mamaki, an ce maharan sun kama wani Kwamandan Birgediya tare da wasu jami’an soji.
Idan har hakan ta tabbata, wannan shi ne karon farko da wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi a Najeriya ta yi nasarar kame Janar din da ke aiki kai tsaye daga fagen fama. A cewar HumAngle, mayakan na ISWAP sun yi wa tawagar sojojin Najeriya kwanton bauna a daren jiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama da kuma jami’an CJTF.
A wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, maharan sun yi awon gaba da wani Birgediya Kwamanda da wasu sojoji. Sai dai har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta bayar da wani martani a hukumance kan harin ba ko kuma tabbatar da makomar jami'in da aka sace.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne SaharaReporters ta ruwaito cewa Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC ya yi Allah-wadai da yawaitar hare-haren ta’addanci a mazabar sa, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da rashin yarda.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kashe manoma hudu a lokacin da suke aiki a gonakinsu a kauyen Kwam, kusa da al’ummar Dille a karamar hukumar Askira-Uba.
Ndume ya bayyana cewa, an kai wa wadanda harin ya rutsa da su hari ne a lokacin da suke girbin amfanin gona, inda ya jaddada tabarbarewar tsaro a yankunan da ke lungu da sakon da ke cikin mawuyacin hali duk da hare-haren da sojoji ke kai wa. "Na damu matuka game da hare-haren da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a sassan mazabana a cikin makon da ya gabata.
Wannan harin ya yi sanadin mutuwar manoma hudu a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a kauyen Kwam, kusa da al'ummar Dille da ke karamar hukumar Askira-uba." Sanatan ya bayyana cewa wadannan kashe-kashen na daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali, domin ‘yan tada kayar bayan sun kara kai hare-hare a wasu al’ummomi.

Comments
Post a Comment