Labrin Jiya A Yau: Shugaban Kasa Ya Gabatar Da Sabon Tsari Domin Tabbatar Da Tsaro
A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, wannan matakin ya biyo bayan sake duba yanayin tsaron kasar ne, wanda hakan ya sa ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar, tare da ba da umarnin kara daukar ma’aikata ga rundunar soji.
Shugaban ya ci gaba da cewa, ‘’Yan sanda da sojoji sun ba su izinin kara yawan jami’ansu, ‘yan sanda za su kara jami’ai 20,000, wanda adadinsu ya kai 50,000. Yayin da a baya na amince da inganta cibiyoyin horar da ‘yan sanda a fadin kasar, wannan bayanin ya baiwa hukumomin ‘yan sanda damar amfani da sansanonin kula da matasa masu yi wa kasa hidima a matsayin wuraren horaswa.
Tinubu ya gargadi ‘yan ta’adda da su guji kalubalantar kudurin gwamnatin sa, ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta fara duba dokokin mu domin baiwa jihohin da ke bukatar ‘yan sandan jihohi damar kafa su.
Ya kuma ba da umarnin cewa jami’an da ake tura su daga aikin ba da kariya ga VIP ya kamata su samu horo cikin gaggawa kafin a tura su yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro.
Shugaban ya kuma kara da cewa, "Hukumar DSS na da izini na ta gaggauta tura dukkan jami'an tsaron dazuzzukan da suka horar da su domin kawar da 'yan ta'adda da 'yan fashi da ke boye a dazuzzukan. An kuma umurci hukumar da ta dauki karin jami'an da za su yi sintiri a cikin dazuzzukan.
"Wannan wani lamari ne na gaggawa na kasa, kuma muna mayar da martani ne ta hanyar kara yawan kasancewarmu a kasa, musamman a yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro. Lamarin ya bukaci kowa ya shiga hannu. A matsayinmu na 'yan Najeriya, dole ne mu shiga tsakani don tabbatar da tsaron kasarmu."
Shugaba Tinubu ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi na ganin an sako ‘yan matan makarantar Kebbi 24 da kuma masu ibada 38 a jihar Kwara.

Comments
Post a Comment