Rigakafi Yafi Magani: Gwamnan Katsina Yayi Abin Da Ya Dace A Lokacin Da Ya Dace.



Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci rufe ilahirin makarantun gwamnati da ke daukacin Garin, bayan wani Mummunan tashin hankali da rahotannin tsaro suka bayyana cewa an samu a wasu yankuna na garin katsinar. 
Wannan babban matakin ya farune bayan taron gaggawa da gwamnatin ta tsara domin tabbatar kare dukkaan rayukan ɗalibai da malamai baki daya.


A wata sanarwar da akayi, gwamnatin jihar ta ayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin habaka da kuma tabbatar matakan kariyar tsaron al'umma, da kuma bai wa manya da kananambhukumomin tsaro don su samu cikkakiyar damar aiwatar da sababbin tsare-tsare na tabbatar da zaman lafiya a kusa da makarantu Gwamnatin baki daya. 


Dikko Rada ya ce rufe makarantun zai kasance na ɗan lokaci ne har sai an kammala sake duba tsaron muhimman wurare. Wannan Matakai da gwamna jihar ya dauka, ya biyo bayan sace 'yan mata ɗaliban makarantun sakandire a jihohin Kebbi da Neja cikin kwanaki kadan da suka gabata, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin hukumomi da iyaye a fadin Arewa maso Yammacin Nijeriya.


Lallai wannan abun a yaba ne, Gwamnan katsinar Dikko Rada hakika yasan aikin shi, yayi abun da ya dace a lokacin da ya dace domin tabbatar da karin al'umman jihar sa musamman Dalibai.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.