Wata Sabuwa: Wasu Gwamnonin PDP Sun Ce "Ya kamata A Tsaida Shugabar Kasa Mace A Zaben 2027

 


2027: Najeriya ta cancanta a samu shugaban kasa mace, mun gaji da ‘yan siyasa da aka sake fada dasu – Inji Uchegbu na PDP Gwamnoni hudu daga jam’iyyar PDP sun isa birnin Ibadan na jihar Oyo, duk da cewa wata babbar kotun tarayya ta dakatar da babban taron jam’iyyar na kasa da aka shirya yi a ranakun Asabar da Lahadi. 


Idan Kuna Da Ciwon Haɗuwa, Karanta Wannan Kafin Ya Shafe! Kamorudeen Ajisafe, Shugaban Jam’iyyar na Kudu-maso-Yamma, ya tabbatar wa da jaridar Punch ranar Juma’a cewa gwamnonin Bauchi, Bala Mohammed; Zamfara, Dauda Lawal; Adamawa, Ahmadu Fintiri; da Oyo, Seyi Makinde, sun riga sun isa Ibadan gabanin taron.


 Kasancewarsu na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar rikicin cikin gida tsakanin bangarorin da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da kuma masu goyon bayan Mukaddashin Shugaban Kasa, Umar Damagum. 


 A gabanin taron, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abuja, yana kalubalantar cire shi daga karbar fom din tsayawa takarar shugaban jam’iyyar na kasa.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.