Yanzu -Yanzu: "Baza Mu Iya Cigaba Da Sa Ido Ba Ana Kashe Kiristoci A Nigeria" Donald Trump .
'Ba Za Mu Zuba Ido Aci Gaba Da Kashe kiristoci A Najeriya Ba'.
Shugaba Donald Trump na Kasar Amurka ya nanata iƙirarin da ya yi cewa ''Kiristoci na fuskantar mummunan barazana a Najeriya".
Yayin wani jawabi da ya gabatar a fadar gwamnatin ƙasar, Mista Trump ya ce Amurka ba za ta ci gaba da zura idanu ana kashe Kiristoci a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
''Masu tsattsauran kishin Musulunci na ci gaba da kashe dubban Kiristoci a Najeriya, kan haka ne na sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake nuna damuwa a kansu''
''A shirye muke don kare ƴan'uwanmu Kiristoci a faɗin duniya'', in ji Trump.
.

Comments
Post a Comment