Yanzu-Yanzu: Sojoiji Sun Dakile Wani Mummunan Harin "Yan Bindiga.


Sojoji Sun Dakile Wani Mummunan harin ‘yan bindiga, sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Kogi.


Rundunar sojojin Najeriya ta 12 da ke Lokoja a jihar Kogi ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kai musu tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su a kusa da Oshokoshoko da Obajana a karamar hukumar Lokoja.


Laftanar Hassan Abdullahi, mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 12 Brigade ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Lokoja ranar Laraba. Ya bayyana cewa, an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Talata, biyo bayan samun bayanan sirrin da ‘yan bindigar ke kai wa a yankin.


 “A ranar 25 ga Nuwamba, 2025, bisa sahihin bayanai dangane da zirga-zirgar ‘yan bindigar kan hanyar Oshokoshoko zuwa Obajana tare da wadanda aka sace, sojojin da ke sansanin ‘yan sintiri na Kabba, tare da hadin gwiwar wasu rundunonin sojan hadin gwiwa, sun gudanar da wani harin kwantan bauna na musamman domin kakkabe masu laifin.


 Sojojin sun yi kwanton bauna inda suka yi artabu da 'yan ta'addar da ke dauke da makamai, wadanda ba a san adadinsu ba.


 ‘Yan bindigar sun bude wuta amma sun samu karfin wuta daga sojojin, lamarin da ya sa suka koma cikin rudani. A yayin arangamar, an kashe ‘yan bindiga guda daya, yayin da wasu suka tsere da raunuka daban-daban na harbin bindiga,” in ji sanarwar.


Kakakin rundunar ya kara da cewa, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kuma ceto daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.


 Ya kara da cewa, "Wanda aka ceto, wanda ya bayyana raunane kuma yana cikin damuwa, ba tare da bata lokaci ba, an kai shi wani wurin kula da lafiya, ana ci gaba da gudanar da ayyuka domin zakulo 'yan kungiyar da suka tsere."

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.