Innalillahi! 'Yan Bindiga Sunyi Wa Sojoji Mummunan Barna A Harin Da 'Yan Ta'addan Suka kai wa Sojoji
A cewar sanarwar, tawagar jami’an tsaron da ta hada da jami’an sojin Najeriya, ‘yan sanda, ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi da ci gaban jihar Kaduna (KADVS) da kuma ‘yan banga na cikin gida, sun je wurin kiwo na gwamnati da ke Kuzuntu.
Sun yi rakiyar ma’aikatan wani kamfanin noma da kuma jami’an yankin domin tantance wuraren kiwo bisa bukatar shugaban karamar hukumar Kubau. "Yayin da suka yi nasarar kammala aikin, an yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a lokacin da suka dawo," in ji Makama. An kashe dan sanda Sunday Ishaya a harin, kuma sojoji da dama sun samu raunuka.
Domin samun sababbin labaran hauusa masu tushe da asali kuyi maza ku garzayo zuwa shfinmu mai suna EagleNewsHausa.

Comments
Post a Comment