Turkashi: Rikicin Addini Ya Barke Tsakanin Crisatan Da Musulmai.
‘Yan majalisar dokokin Amurka da wata hukumar ‘yancin addini na taruwa zasu tattauna kan zargin kisan kiyashin da ake zargin Kiristoci a Najeriya.
Taron da ke tafe na da nufin tattara muhimman shaidu da za su taimaka ga cikakken rahoton da shugaba Trump ya bayar game da kashe-kashen Kiristocin Najeriya.
A ranar Talata ne kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin Amurka da kwamitin kula da harkokin kudi za su yi wani taron hadin gwiwa tare da hukumar kare hakkin addini ta Amurka domin bayyana batutuwan da suka shafi kisan kiyashin da ake zargin Kiristoci a Najeriya.
Shugaban kwamitin Tom Cole ya bayyana cewa mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar kuma shugaban kwamitin tsaro na kasa Mario Díaz-Balart tare da sauran mambobin kwamitin za su gana da hukumar kare hakkin addini ta Amurka da masana daban-daban domin magance karuwar tashe-tashen hankula da musgunawa Kiristoci a Najeriya.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, taron zai tattara muhimman shaidun da za su taimaka wajen samar da cikakken rahoton da shugaba Trump ya jagoranta, da ke mai da hankali kan kisan gillar da aka yi wa Kiristocin Najeriya da kuma matakan da Majalisar za ta iya dauka na taimakawa fadar White House wajen kare al’ummomin addinai masu rauni a duniya.

Comments
Post a Comment