Yanzu-Yanzu: An Bankado Mummunan Asirin Wasu Manyan 'Yan Siyasa A Nigeria.
Tsohon babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Lucky Irabor ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa a Najeriya na da hannu wajen ba da tallafin ta’addanci da kuma amfani da rashin tsaro domin cimma muradun siyasa.
Sababbin labaran hauusa a yau Yan siyasan Nigeria, Asirin yan siyasa, Hausa, Political scandal Nigeria/
Irabor ya bayyana haka ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV, a Siyasar Yau, inda ya yi jawabi game da karuwar bukatar gwamnatin tarayya na bayyana sunayen wadanda ke tallafawa ayyukan ta’addanci.
Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wata sanarwa da Daniel Bwala, mashawarci na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin sadarwa ya yi a baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta bayyana sunayen masu kudin ta’addanci kuma tuni aka fara aiwatar da wasu muhimman ayyuka.
Irabor, wanda ya jagoranci sojojin kasar daga shekarar 2021 zuwa 2023, ya lura da cewa da gangan wasu ‘yan siyasa ke amfani da rashin tsaro wajen yada labaran karya da ke goyon bayan burinsu na siyasa.
Domin samun sababbin labaran n hausa ku bi biyi shafin mu Eagle 🦅News Hausa
Kusa mana ra'ayin ku a kasa

Comments
Post a Comment