Posts

Showing posts from July, 2024

Inalillahi! An kashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Gaza😭😭😭

Image
An kwashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Ga. Mazauna Gaza Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kwashe wasu FalasÉ—inawa da suka ji raunuka da kuma marasa lafiya daga Gaza zuwa HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa don neman magani. Wannan ne yunÆ™uri mafi girma na aikin kwashe majinyata da aka yi tun bayan fara yaÆ™in sakamakon harin da Hamas ta kai a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.  Majiyoyi a Gaza sun rawaito cewa an kwashe majinyata 150 cikin bas-bas biyar, amma har yanzu WHO ba ta tabbatar da asalin marasa lafiyan ba. Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza sun gurgunta fannin kiwon lafiyar yankin. Kuma an rufe babbar hanyar da ake bi domin kwashe marasa lafiya ta kan iyakar Gaza da Masar a Rafah bayan da sojojin Isra'ila suka karÉ“e iko da mashigar a farkon watan Mayu. WHO ta ce kawo yanzu kimanin Æ´an Gaza 5,000 ne suka samu kulawa a asibitoci da ke wajen yankin, amma har yanzu wasu 10,000 na buÆ™atar barin Æ™asar domin neman lafiya.  Tun kafin É“arkewar yaÆ™in wasu mazauna Ga...

Yanzu-Yanzu: Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshin Sa Dake Nigeria.

Image
Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshinsa Da ke Faɗin Najeriya A Yau Talata. Matakin kamfanin ba ya rasa nasaba da yadda wasu abokanan hulɗarsa da aka rufewa layin waya suka yi cincirindo a ofisoshin kamfanin har ma wasu suka yi ƙoƙarin kutsa kai don neman a buɗe masu layukan nasu. MTN ya rufe layukan mutane saboda sun gaza haɗa lambarsu ta ɗan ƙasa da layinsu. MTN ya wallafa sanarwar rufe ofisoshin nasa a shafinsa na X inda ya ce "ku sani cewa ofisoshinmu a faɗin Najeriya za su kasance a rufe yau 30 ga watan Yulin 2024.

Da Dumi-Dumi: 'Ƴan Ta’adda 284 Sun MiÆ™a Wuya Ga Sojojin HaÉ—aka

Image
Ƴan Ta’adda 284 Sun MiÆ™a Wuya Ga Sojojin HaÉ—aka. Nasarar yaki da ta’addanci na ci gagaba da samuwa, domin a tsakanin 10 zuwa 17 ga Yuli, 2024, mayakan Boko Haram 284 tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar hadin Gwuiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a Kamaru.  Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, Shugaban sashen Hulda da Jama’a, ya bayyana cewa dakarun sashi na 1 sun karbi mayaka biyar a Wulgo a ranar 11 ga Yuli, 2024. Bayanai na farko sun nuna cewa wadannan mayakan sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar kukumar Marte ta Jihar Borno, Nijeriya. A wannan ranar, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50 da ya tsere daga maboyar Jibilaram, ya mika wuya ga dakarun. Haka zalika, mayaka 19 sun mika wuya a Madaya, Arewa Maso Gabashin Kamaru, da wasu 11 a Wulgo.  A ranar 12 ga Yuli, mayaka 64, ciki har da manya shida, mata 20, da yara 38, sun mika wuya a Bonderi, Kamaru. An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun MiÆ™a Wuya Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa ...

Rikicin Masarautar Kano: Gmamtin Abba Kabir Yusuf Ta Sauya Alkibila

Image
Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla . A wani lamari na sauya sabon salo dangane da rikicin sarautar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake maido da masarautu uku daga cikin hudu da ya rushe. A rana daya Majalisar Dokokin Kano ta gabatar da kudirin samar da dokar kirkirar masauratun masu daraja ta biyu, aka yi mata karatun da ya kamata, aka zartar da dokar, sannan aka kai wa gwamna kuma ya rattaba mata hannu da yammacin ranar Talata. Bayan gwamna ya rattaba wa dokar hannu, nan take kuma ya amince da nadin sabbin sarakuna masu daraja ta biyu da suka hada da masarautun Gaya, Rano da Karaye. Gwamnan ya nada Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Rogo. Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Bunkure, sannan kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda shi ne tsohon Sarkin Gaya. Wannan mataki na gwamnatin Jihar K...

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Amince Da Maki 140 Zuwa 100 Mafi Karancin Maki Domin Shiga Manyan Makrantu.

Image
. JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu. Labarai Masu Nasaba Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu Da Kashi 50 Cikin 100 Gwamnatin Kaduna Ta Nisanta Kanta Akan Bidiyon Dukan Dan Balki Kwamanda . Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 a matsayin mafi karancin maki na shekarar 2024 da za a iya shiga jami’o’in kasar nan. Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan bayar da takardar shiga manyan makarantu a shekarar 2024. Malamin Tsangaya Ya Shiga Hannu Kan Zargin Luwadi Da ÆŠalibai A Jigawa Da ÆŠumi-É—umi: Gwamnatin Tarayya Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Amince A Kan N70,000 Mafi Ƙarancin Albashi Oloyede ya ce, an amince da 100 a matsayin mafi karancin maki a Kwalejin Kimiyya da Kwalejojin Ilimi. Farfesa Ishaq ya bayyana cewa, wadannan mafi karancin maki da aka bayyana, su ne mafi Æ™anÆ™antar maki, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomin manyan makara...

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Fara Bai Wa Ma'aikata Bashin Kudin Noma.

Image
Gwamnatin Jigawa Ta Ƙaddamar Da Bai Wa Ma'aikata Bashin KuÉ—in Noma. Gwamnatin jihar Jigawa a raewacin Najeriya ta Æ™addamar da shirin tallafa wa ma'aikata a É“angaren noma. Shirin ya tanadi bai wa ma'aikatan gwamnati bashi ta yadda za su iya bayar da tasu gudunmawa wajen noma wasu zaÉ“aɓɓun amfanin gona. Shirin bayar da bashin zai samar da tallafin kayan aikin gona da kuÉ—in aiki don noma amfanin gona kamar shinkafa, da riÉ—i, da gero, da kuma dawa, inda ake fatan ma’aikatan za su biya bashin bayan kammala girbi. Hukumomin jihar sun ce sun É“ullo da shirin ne la’akari da halin matsi da kuma tsadar rayuwa, ta yadda hakan zai bai wa ma’aikata damar noma abin da za su ci da kuma samun kuÉ—i. Shugaban Ma'aikata Muhammad Kandira Dagaceri, shi ne shugaban kwamitin da ke kula da shirin bayar da bashin kuma ya ce sun buÉ—e wani shafi a internet inda ma’aikaci zai yi rajista. "Yanzu mun fara da ma'ikata 8,432 a kashin farko," in ji shi. 

Fifikon Manzon Àllah SAW Da Halittu Darasi Daga suratur Najmi.

Image
Fifikon Manzon Àllah SAW Da Halittu Darasi Daga suratur Najmi  Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Idan ba a manta ba a karatunmu nFifikon Manzon Allah SAW: Darasi Daga Suratun Najmi (2)a makon da ya gabata mun tsaya ne a kan ayoyin da Manzon Allah (SAW) ya gani a lokacin da ya yi Mi’iraji. Isara’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW) duka suna nuna mana girman darajarsa ne a wurin Allah Tabaraka wata’ala. A Mi’iraji, Manzon Allah (SAW) ya ga Rafrafu, ya ga Jibrilu, ya ga Al’arshi, ya ga Kursiyyu, ya ga Magaryar Tikewa, ya ga Mustawad Darafaini (wani irin waje ne da misali idan ka yi kudu sai ka fito yamma, idan ka yi sama sai ka fito kasa, abu ne da ya fi karfin hankali). Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2) Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1) To amma me ya sa aka ce Manzon Allah ya ga wani bangare ne daga cikin ayoyin Ubangijinsa? Domin kamar yadda ayar ta ce “lakad ra’a min…”, ita “min” tana nuna wani bangare ...

Rikicin Sarakuna: Tube Sarakunan Arewa Ba Mafita Bane

Image
‘ Rikicin Tube Sarakuna Bala’i Ne Ga Arewa’ Wani Masanin Tarihin Masarautun Gargajiya da Diflomasiyya a Jihar Kaduna, Alhaji Usman Dalhatu ya bayyana cewa; cire sarakuna wata babbar masifa ce da ke fuskantar Arewacin Nijeriya, duk da cewa irin wannan rikici ba wani sabon abu ba ne, lamarin ne wanda ke da asali tun a lokacin Turawan mulkin mallaka. Dalhatu, wanda marubucin tarihi ne; sannan kuma makusanci ga marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya bayyana cewa; muddin gwamnoni suka ci gaba da yi wa masarautun gargajiya karen-tsaye, ko shakka babu sun dauko hanyar ruguza Arewacin Nijeriya, musamman ganin yadda sarakunan ke bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da kuma hadin kan al’umma baki daya. Marubucin Tarihin ya bayyana haka ne, a zantawarsa da wakilinmu a Kaduna; inda ya fara da shimfida kan tarihin rikicin sarakunan da kuma Turawan Mulkin Mallaka. “Wannan rikici na masarautun gargajiya da gwamnoni, bala’i ne da ke shafar Arewa a halin yanzu, wanda Turawan Mulkin Mallaka su...

Da Dumi-Dumi: Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Ganawar Sirri Da Gwamnoni.

Image
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shettima, Da Gwamnonin Na Ganawar Sirri. A halin yanzu shugaba Bola Tinubu na wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni a ofishinsa da ke fadar gwamnatin tarayya a ranar Alhamis. An fara ganawar ne bayan da shugaban ya kammala tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadagon, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata. Noma: Gwamnan Zamfara Ya Nemo Masu Zuba Jari Daga Ƙasar Turkiyya Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Yari Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara; Charles Soludo na Jihar Anambra da Usman Ododo na Jihar Kogi. Ya zuwa yanzu dai ba a san makasudin taron ba, amma yana zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kotun kolin ta yanke hukunci kan bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Wutar Lantarki Gidan Gyaran Hali.

Image
Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Yari. Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman a gidan yari na Kuje da ke Abuja har sai an duba bukatar belinsa. Kotu ta yanke hukuncin tura tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, gidan yari, wanda ya yanke jiki ya fadi lokacin da ake zaman kotun. Sin Ta Gabatar Da Takardar Bayani Kan Yadda Take Kiyaye Muhallin Halittun Teku.   Jawabin Muller Kan Yin Ritaya Daga Bugawa Kasar Jamus Kwallo A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, mai shari’a James Omotosho, ya bayar da umarnin ne, biyo bayan gurfanar da Mamman a kotun kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi halasta kudaden haram. Alkalin kotun ya sanya ranar Juma’a 12 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraren karar neman belinsa. Bugu da kari, alkalin ya bayar da umarnin a tsare wanda ake kara a gidan yari na Kuje har sai an saurari karar. Labarai Masu Nasaba Albashi: Shugabannin Kungiyoyin Kwadago Na Gana Wa Da T...

Da Dumi-Dumi: Kotun Jihar Kebbi Ta Tuhuma CSP Rano Akan Zargin Kudi Sama Da Mikyan 37 Naira.

Image
Badakalar Kudade Fiye Da Miliyan 37: Kotu A Kebbi Ta Umarce CSP Rano Ya Nemo Shaidun Kare Kansa. Alkaliyar Babbar Kotun Jihar Kebbi ta biyu, Mai shari’a Nusurat Ibrahim, ta sanya ranar 24 ga Yuli, 2024, ga CSP Abdullahi Bala Rano da ya gabatar da shaidu don kare kansa kan zargin karya yarjejeniyar kasuwanci. Wani dan kasuwa mai suna Bashar Ibrahim da wasu mutane hudu ne suka maka CSP Abdullahi Bala Rano a gaban kotu inda suka nemi Kotun da ta tilastawa wanda ake kara ya biya kudaden kamar yadda yarjejeniyar kasuwancinsu ta tanada. Da ÆŠumi-É—umi: Kotun Ƙoli Ta Ba Ƙananan Hukumomi ‘Yancin Cin Gashin Kansu Sheikh Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa A cikin takardar karar, masu karar sun sanar da Kotu cewa, akwai dangantaka ta Kasuwanci a tsakaninsu da wanda suke kara, bayan sun amince da gudanar da Kasuwancin Manja inda suka zuba jari a hannun CSP Abdullahi Bala Rano da ke aiki da rundunar ‘yansanda ta jihar Kebbi. A zaman kotun da ke Birnin K...

Sheikh DAurawa Yayi Kira Ga ÆŠaukacin Muslimai; Dasu Guji Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa.

Image
Sheikh Aminnu Ibrahim Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa. Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su guji gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar nan. Ana shirin gudanar da zanga-zangar na kwanaki 10 domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta sakamakon hauhawar farashin man fetur, hauhawar farashin kayayyakin abinci, rashin tsaro da dai sauransu. Ma’aikatan Ruwa Na Jihar Kaduna Sun Yi Zanga-zangar Rashin Albashi. Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta. Amma a hudubar da Sheikh Daurawa ya gabatar a Kano a Juma’ar da ta gabata, ya yi nuni da cewa zanga-zangar tana da illa fiye da alherinta, kuma bai kamata a karfafa mata gwiwa ba. Ya ce, “Ba ma goyon bayan zanga-zangar saboda mun ga abin da ya faru a Siriya, Sudan, Libya da Iraki. “WataÆ™ila za a gudanar da zanga-zangar ne da kyakkyawan n...

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Tura Mutumin Da Yayi Yin kurin kurin Hallaka Kansa Zuwa Gidan Mahaukata.

Image
‘ Yansanda Sun Tura Mutumin Da Ya So Kashe Kansa Zuwa Gidan Mahaukata. ‘Yansanda sun tura Shuaibu Alhaji Yushau, wanda ya hau karfen gidane rediyo a yankin Katampe da ke Abuja domin kashe kansa a ranar Litinin saboda matsin rayuwa, zuwa gidan mahaukata domin duba lafiyarsa. ‘Yansanda sun tsare Yushau a babban birnin tarayya, bayan an yi nasara ya sauko daga kan karfen gidan rediyon da yau da nufin hallaka kansa. Adadin Wadanda Suka Mutu A Yakin Gaza Da Isra’ila Ya Kai 38,000. Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa Ganau, ya bayyana cewar matakin da Yushau ya dauka ya haifar da rudani a yankin. An sanar da ‘yansanda lamarin, abin da ya sa suka yi gaggawar zuwa wajen tare da tattaunawa da shi har ta kai ga ya sauko. Kakakin ‘yansandan babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, a ranar Talata ta bayyana cewar za a gudanar da shi tare da tuhumarsa kan kokarin aikata kisan kai. Labarai Masu Nasaba Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar ...

Da ÆŠumi-ÆŠumi: Shugaba Bola Tinubu, Ya Taya Sheikh Dahiru Usaman Bauchi Murnanr Cika Shekara 1000 A Duniya

Image
Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekara 100 Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya babban malamin addinin musulunci Shiekh Dahiru Bauchi murnar cika shekara 100 a duniya. A sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Bola Tinubu ya bayyana Shehin malamin a matsayin wani haske da ya yi wa addinin musulunci hidima da kuma yin tasiri ga tarbiya da tsari a Najeriya Ya kuma gode wa babban malamain na darikar Tijjaniyya kan sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimi da kuma tasiri ga rayuwar ƴan Najeriya. Shugaba Tinubu ya yi addu'ar ƙoshin lafiya da ƙarin hikima ga malamin.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wani Matashi Yayi Barazanar Faɗowa Daga Babban Ƙarfen Gidan Redon Abuja.

Image
Wani Matashi Ya Yi Barazanar FaÉ—owa Daga Dogon Ƙarfen Gidan Rediyo A Abuja. Labarai Masu Nasaba Wani Alhaji Daga Zamfara Ya Mayar Da MaÆ™udan KuÉ—aÉ—en Da Ya Tsinta A Makkah Dan Kasar Zimbabwe Ya Aure Mahaifiyarsa Bayan Ya Yi Mata Ciki Wani matashi mai suna Shu’aibu Alhaji Yusuf ya yi barazanar faÉ—owa daga tsanin gidan rediyon Aso da talabijin dake kan tsaunin Katampe a Babban Birnin Tarayya (FCT) a yau Litinin, matuÆ™ar idan Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da tallafin mai da kuma magance matsalolin tsaro a Nijeriya ba. Yusuf, wanda É—an asalin Maiduguri ne a Jihar Borno, ya bayyana buÆ™atunsa a rubuce a kan wata kwalba kafin ya hau saman tsanin. Yusuf ya buÆ™aci a ayyana dokar ta baci a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna, Neja, da Borno saboda rashin tsaro, yana kira da a É—auki matakin gaggawa don kawar da ‘yan ta’adda a yankunan. Har ila yau, ya nemi gwamnati ta buÉ—e kan iyakoki domin shigo da abinci don yaÆ™ar karancin abinci da kuma magance Æ™aruwar yaran da ba sa zuwa makaranta. ...

Babban Abin Da Ya kawo Ƙarancin Man Fetur A Najeriya-NNPCL

Image
  Abin Da Ya Da Yakawo Ƙarancin Fetur A Najeriya - NNPCL Kamfanin man fetur na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce ambaliyar ruwa da kuma rashin kyawun yanayi ne suka jawo tsaiko wajen man a Abuja da wasu jihohin Æ™asar. Tun a makon da ya gabata ne aka fara ganin dogayen layuka a Æ™ofar gidajen mai na Abuja babban birnin Æ™asar da kuma wasu jihohi, inda masu ababen hawa kan shafe awanni kafin su sha man. Wata sanarwa da NNPCL ya fitar ta ce "hakan ta faru ne sakamakon matsalar jigilar sauke man daga manya zuwa Æ™ananan jiragen ruwa na dako". "Haka nan, saboda hatsarin da ke tattare da fetur da kuma bin umarnin hukumar kula da yanayi cewa kada a yi jigilar mai yayin da ake tsaka da kwarara ruwan sama, ba zai yiwu a yi lodin mai ana tsaka da tsawa da walkiya da kuma shatata ruwa ba," in ji sanarwar. "Bugu da Æ™ari, matsalar ta ta'azzara ne saboda ambaliya ta mamaye hanyar manyan motoci, abin da ya jawo tsaiko a jigilar man daga tashohin ruwa zuwa Abuja." Zagayen d...

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Daga Shari'ar Matashin Da Ya ƙone Masallata A Kano.

Image
Kotu Ta Dage Shari’ar Matashin Da Ya Kone Masallata A Kano. Kotu ta dage shari’ar Shafiu Abubakar, wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar wasu masallata 19, a garin Gadan da ke karamar hukumar Gezawa a Jihar Kano.  An dage zaman ne sakamakon rashin kara sunayen mutanen da suka mutu sakamakon lamarin. Kenya Ta Dakatar Da Yi Wa Ma’aikatan Gwamnati Karin Albashi JAMB Ta BankaÉ—o ÆŠalibai 3000 Da Suka Kammala Karatun Bogi An ruwaito cewar cewa, matashin mai shekaru 38, mazaunin kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa, na fuskantar shari’a a babbar kotun Kano da ke Rijiyar Zaki. Tun da farko dai an zargi Abubakar da cinna wa wani masallaci wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 14 tare da raunata wasu da dama. Sai dai mai gabatar da kara, karkashin jagorancin daraktan masu gabatar da kara (DPP) na ma’aikatar shari’a ta Jihar Kano, Barista Salisu Tahir, ya sanar da kotun cewa adadin wadanda suka mutu ya karu daga 14 zuwa 19 saboda haka ya bukaci karin lokaci don sabunta takardar t...

Inalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Matar Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Tarasu

Image
Àllah Yayi Wa Hajiya Zainab Rasuwa Matar Mataimakin Gwamnan Jihar Neja . Mutanen Da Suka Mutu A Harin Ƙunar BaÆ™in-Wake A Wajen Bikin Aure Ya Ƙaru Zuwa 18 A Borno. Hajiya Zainab Garba, matar mataimakin gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, ta rasu. Ta rasu ne a ranar Talata a wani asibiti da ke Minna bayan ta yi fama da gajeriyar jinya. Farashin Man Fetur Ya Kai Naira 937 Kan Kowace Lita A Jigawa.  Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda A cikin sakon ta’aziyyar da babban sakataren yada labarun gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ya fitar, ya yi alhinin rasuwarta, inda ya bayyana hakan a matsayin babban rashi ga jihar. Gwamna Bago, ya yi addu’ar Allah ya jikanta da kuma fatan Allah ya sa Jannatul-Firdaus ce makomarta.

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Ceto Mutum 3 Daga Wani Gini Da Yarushe A Abuja .

Image
An Ceto Mutane 3 Daga Wani Gini Da Ya Rushe A Abuja – ‘Yansanda. Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja, ta tabbatar da rushewar wani gini mai hawa hudu ne a yankin Garki. Sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce ginin ya rushe ne ranar Litinin da daddare. Mutane 20 Sun Mutu, 52 Sun Ji Rauni A Harin Bam A Borno – DHQ Kwastam Ta Kama Bindigu A Tashar Jiragen Ruwa A Ribas Ta ce bayan samun kiran waya kan lamarin, kwamishinan ‘yansandan Abuja, Benneth Igweh, ya tura jami’ansa zuwa wurin. A cewar sanarwar, an kubutar da mutum uku daga cikin ginin da ya rushe, inda kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa da lafiyarsu. Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta ankarar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Æ™asa domin su É—auki ragamar zaÆ™ulo mutanen da Æ™asa ta birne. Labarai Masu Nasaba Mutane 20 Sun Mutu, 52 Sun Ji Rauni A Harin Bam A Borno – DHQ. Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniyar Yakar Yunwa Da Saudiyya Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa an sanar da H...

Inalillahi! Ànyi Wani Mummunan Hatsarin Mota A Jihar Kano Mutane Da Dama Sun Rasu Wasu Kuma sun Jikkata

Image
An Sake Wani Mummunan Hatsarin Mota A Kano, Mutane 25 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata . Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kano ya laÆ™ume rayukan mutane 25 da sanyin safiyar yau Litinin bayan da wata motar tirela ta yi hatsari a gasar sama ta Dangwaro da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya. Motar mai É—auke da fasinjoji 90 tare da dabbobi, babura, da buhunan masara ta kife. Hakan ya biyo bayan wani hatsari makamancin haka a ranar Juma’ar da ta gabata a Æ™aramar hukumar Kura, inda wata tirela ta kutsa kai cikin masu ibada juma’a, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14. Kakakin hukumar kiyaye haÉ—É—ura ta kasa (FRSC), Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa mutane 53 ne suka samu raunuka a hatsarin, yayin da wasu 12 suka samu raunuka. Gwamnatin Kano Ta Musanta Bullar Cutar Kwalara A Jihar Gwamna Abba Ya Nuna Damuwarsa Kan Halin Da Ya Samu Hukumomin KAROTA Da REMASAB Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 3:30 na dare, kuma an alaÆ™an hatsarin da gudun wuce sa’a da kuma rashin kula da direban tirelar ...