Da Dumi-Dumi: Tsohon Gwamnan Kogi Yahayya Bello Zai Gabatar Da kansa A Gaban Kotun.
Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni Bayan kai ruwa rana, daga karshe dai tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince ya mika kansa a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ranar 13 ga watan Yuni kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) take yi masa kan almundahanar makudan kudade. Lauyan da ke tsayawa, Yahaya Bello, Abdulwahab Mohammed, ya yi wa mai shari’a Emeka Nwite, alkawari a ranar Juma’a, bayan kotun ta ki amincewa da bukatar dakatar da shari’ar da wanda ake kara ke yi. Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo, Zan Yi Murabus Matukar Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba Shugaban EFCC. Muhammad ya ce tsohon gwamnan baya tsoron a gurfanar a gaban kotu ko kadan. Lauyan tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa, rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana a Abuja, ...