Posts

Yanzu-Yanzu: An Bankado Mummunan Asirin Wasu Manyan 'Yan Siyasa A Nigeria.

Image
 Tsohon babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Lucky Irabor ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa a Najeriya na da hannu wajen ba da tallafin ta’addanci da kuma amfani da rashin tsaro domin cimma muradun siyasa. Sababbin labaran hauusa a yau Yan siyasan Nigeria, Asirin yan siyasa, Hausa, Political scandal Nigeria/ File picture of ex-general Irabor Irabor ya bayyana haka ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV, a Siyasar Yau, inda ya yi jawabi game da karuwar bukatar gwamnatin tarayya na bayyana sunayen wadanda ke tallafawa ayyukan ta’addanci. Kalaman nasa sun zo ne a matsayin martani ga wata sanarwa da Daniel Bwala, mashawarci na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin sadarwa ya yi a baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta bayyana sunayen masu kudin ta’addanci kuma tuni aka fara aiwatar da wasu muhimman ayyuka. Irabor, wanda ya jagoranci sojojin kasar daga shekarar 2021 zuwa 2023, ya lura da cewa da gangan wasu ‘yan siyasa ke amfani da...

Turkashi: Rikicin Addini Ya Barke Tsakanin Crisatan Da Musulmai.

Image
‘Yan majalisar dokokin Amurka da wata hukumar ‘yancin addini na taruwa zasu   tattauna kan zargin kisan kiyashin da ake zargin Kiristoci a Najeriya. Taron da ke tafe na da nufin tattara muhimman shaidu da za su taimaka ga cikakken rahoton da shugaba Trump ya bayar game da kashe-kashen Kiristocin Najeriya.  A ranar Talata ne kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin Amurka da kwamitin kula da harkokin kudi za su yi wani taron hadin gwiwa tare da hukumar kare hakkin addini ta Amurka domin bayyana batutuwan da suka shafi kisan kiyashin da ake zargin Kiristoci a Najeriya.  Shugaban kwamitin Tom Cole ya bayyana cewa mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar kuma shugaban kwamitin tsaro na kasa Mario Díaz-Balart tare da sauran mambobin kwamitin za su gana da hukumar kare hakkin addini ta Amurka da masana daban-daban domin magance karuwar tashe-tashen hankula da musgunawa Kiristoci a Najeriya.  Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, taron zai tattara muhimman ...

Da Dumu-Dumi: Abun Da Aka Boye Game Da Sheik Dahiru Usman Bauchi

Image
Sheik Dahiru Usman Bauchi An haifeshi a 1927/28 ga watan june, yayi wafati 2025, ,26 ga Nuwamba. Mahaifiyarsa 'yar garin Gwambe state ne, hakanan dab garin Bauchi ne kuma bababnsa babban malamine mahadadcin Qur'an. Sheik Dahiru  ya fara karatu wajan ma haifinsa har ya haddace allqur'ani mai girma wajan babansa tun yana dan Shekara goma saha tara (19). Babansa yaturashi yanemi ilimi yafara zuwa jiha-jiha domin neman ilimi can sai Allah ya bayyana Sheik Ibrahim sai shehu yashiga cikin tafiyar Sheik Ibrahim Abdullahi inyass, ya zama almajirin shehu shine malamin Shehk Dahiru Na karshe.  Sheik Dahiru Usman Bauchi yazama babban jaogra na darika tijjaniyya har ya Kai Sheik Ibrahim yace mashi "kaje Ka fadi duk abun da ka fada ni na fada" Shehk Dahiru yana alfahri da wannan sosai na kasancewarshi almajirin Shehk Ibrahim Inyass. Har sai da yazama babban masanun ma'arufa, tafsir da qur'ani mai girma. Sheikhul Islam Sheik Dahiru Usman Bauchi yayi ma addini hidima mat...

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Image
La'ilaha Illalahu Muhammadu Rasulillahi Salallahu Alaihi Wasallama. Kamar yadda kuke gani Kai tsaye daga jihar Bauchi wajen da za ayi jana'izar maulan Sheik Dahiru Usman Bauchi. Wallahi duk wnada yatsaya ma Allah zai tsaya mai bama kawa Dan Allah dubu taron dandazon al'umma duk sun tarune domin gabbatar da jana'izar maulana a wani babban masallacin idi dake Bauchi. Allah ubangiji yabamu albarkarsu tadu tayi kyau Allah ka Karbi bakuncinsa kayi mashi kyakyawan masauki ka hadashi da manzon rahama

Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un!!! Allah Yayi Wa Sheik Dahiru Usman Bauchi Rasuswa

Image
Innalillahi Wa inna ilaihi raji'um!!! Innalillahi Wa inna ilaihi raji'um!!! Allah ya Yayi wa babban malamin addinin Islama kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 101 a duniya, a lissafin kalandar Musulunci. Innalillahi Wa inna ilaihi raji'um!!! Allah ya Yayi wa babban malamin addinin Islama kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 101 a duniya, a lissafin kalandar Musulunci. Rahotanni Sun ruwaito cewa shehun malamin ya rasu a daren da ya gabata na laraba kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar Majiyar ta kuma ce za'a sanar da lokacin jana'izar malamin nan gaba kadan. .

Labrin Jiya A Yau: Shugaban Kasa Ya Gabatar Da Sabon Tsari Domin Tabbatar Da Tsaro

Image
Tinubu ya ba da sanarwar gaggawar tsaro da kuma shirin daukar ma'aikata sosai a Sojoji da 'Yan Sanda.  Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta-baci dangane da matsalar tsaro a Najeriya, inda ya jaddada bukatar mayar da martani mai karfi kan sabbin barazana a fadin kasar.  A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, wannan matakin ya biyo bayan sake duba yanayin tsaron kasar ne, wanda hakan ya sa ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar, tare da ba da umarnin kara daukar ma’aikata ga rundunar soji.  Shugaban ya ci gaba da cewa, ‘’Yan sanda da sojoji sun ba su izinin kara yawan jami’ansu, ‘yan sanda za su kara jami’ai 20,000, wanda adadinsu ya kai 50,000. Yayin da a baya na amince da inganta cibiyoyin horar da ‘yan sanda a fadin kasar, wannan bayanin ya baiwa hukumomin ‘yan sanda damar amfani da sansanonin kula da matasa masu yi wa kasa hidima a matsayin wuraren horaswa.  Tinubu ya gargadi ‘yan ta’adda da su guji kalubalantar kud...

Wata Sabuwa: Babbar Kungiyar Kwallon Kafa Zata Saida 'Yan Wasa Kimanin Goama.

Image
Rahotanmu  Na Yau sun bayyana cewa Manchester United na neman siyar da ‘yan wasa 11 na rukunin farko da suka hada da kaftin Bruno Fernandes da mai tsaron baya Harry Maguire, a matsayin wani bangare na sake fasalin kungiyar da aka shirya yi a bazara na shekara ta 2026.  Duk da kokarin da Ruben Amorim ya yi, wasan kungiyar bai samu ci gaba ba, wanda hakan ya sa suka makale a tsakiyar teburi ba tare da wata fayyace hanyar ci gaba ba. Fernandes na iya kasancewa cikin wadanda za su bar kulob din a bazara.