Yanzu-Yanzu: "Yadda Za A Magance Rashin Tsaro A Nigeria," Daga Bakin Kodinaitan Arewa
Hanya Mafi Sauki Da Za A Magance Matsalar Tsaro A Katsina Gamayyar Kungiyoyin Arewa. Babban kodinaita na gamayyar kungiyoyin arewa na Jihar Katsina, Habibu Ruma ya bayyana wasu hanyoyi da suke ganin idan gwamnatin Jihar Katsina ta yi amfani da su za a iya samun nasara kan matsalar tsaron da ta addibi jihar da yankin arewa baki daya. Kodinaitan gamayyar kungiyoyin ya yi wannan karin haske ne a lokacin da suka shirya wani taro domin fadakar da ‘ya‘yan kungiyar halin da yanayin da tsaro ya samu kanshi a Jihar Katsina da kuma arewa baki daya. Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kan. Mun Dukafa Kawo Karshen Matsalar Wuta A Arewa Maso Gabas – Gwamna Inuwa .Habibu wanda ya yi bitar cewa matsalar tsaro a Jihar Katsina da kuma arewacin Nijeriya ta kassara duk wani ci gaba a bangaren ilimi da haifar da jahilci da rashin shugabanci da shan miyagun kwayoyi wanda har gobe sune ake gani matsayin dalilin faruwar haka. Yana mai cewa farmakin da ‘yan bindiga...