Posts

Showing posts from June, 2024

Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani

Image
Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani Hukumar kididdiga ta kasar Saudiyya GASTAT ta fitar da cikakkun alkaluman da suka shafi aikin hajjin shekarar 2024, inda ta bayyana cewa alhazai 1,833,164 ne suka gudanar da aikin hajjin bana a Makka. Wanda hakan ya nuna yadda Alhazai dabam-dabam daga sassan duniya suka halarci aikin Hajjin Bana. A bangaren jinsi a tsakanin Alhazan wannan shekarar, an samu maza 958,137 da mata 875,027 a gaba ki dayan Alhaza da suka gabatar da ibadar. Mafiya yawa daga cikin mahajjatan da adadin da sun ya kai 1,611,310, sun fito ne daga kasashen ketare, yayin da 221,854 suka kasance mahajjatan cikin gida ‘yan kasar Saudiyya. Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya, Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG. Kason Nahiyoyin Da Suka Halarci Kasar Saudiyya Kididdigar alkalumman yawan mahajjatan bana ta nuna kashi 63.3% na mahajjatan Asiyawa ne (wadanda suka fito daga yankin Asiya) wadanda ba Larabaw...

Yanzu-Yanzu: 'Ƴan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Shahararan Mawaƙin Nan Dauda Kahutu Rarara

Image
' Ƴan Bindiga' Sun Sace Mahaifiyar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara  Hukumomi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da sace mahaifiyar sanannen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara. A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Mu'azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma'a a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja. Mu'azu ya ce wadanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami'an da ke tsaron gidan sun sani ba. Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami'an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ƴan bindigan Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.  Hakan ya durƙusar da sana'o'i da harkoki na yau da kullum.

Da Dumi-Dumi: Rikici Ya Ɓarke A Yayin Da Akai Arangama Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Jihar Jigawa.

Image
Mutane 3 Sun Jikkata Yayin Da Manoma Da Makiyaya Suka Yi Arangama A Jihar jigawa . Akalla mutane uku ne suka jikkata yayin da manoma da makiyaya suka yi arangama a dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa. Kakakin rundunar DSP Lawal Shiisu ne, ya tabbatar da hakan a jihar a ranar Alhamis. Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro. Ana Ganawa Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya. “Mun samu labarin faruwar lamarin a ranar Talata, da misalin karfe 2:15 na rana,” in ji kakakin. “Da samun rahoton, jami’in ‘yansanda na sashen Kiyawa, tare da tawagar ‘yan sintiri, suka garzaya wajen. Tawagar ta hada da jami’an karamar hukumar Kiyawa, shugabannin Kautal Hore da Miyetti Allah, kungiyar manoman Nijeriya (AFAN), da shugabannin kauyen da abin ya shafa. “A yayin tattaunawa a tsakanin masu ruwa da tsaki, rundunar ta gano mutane uku da suka jikkata tare da ceto wasu shida da ake shirin kai wa hari,” in ji shi. Labarai Masu Nasaba Gwamnatin Kano Za Ta...

Inalillahi! Sojojin Isra'il Da Yawa Sun Rasa Ransu A Sakamakon Tashin Bam

Image
Bam Ya Kashe Sojan Isra'ila A Gaɓar Yamma Wani sojin Isra'ila yace mutum 16 sun rasa rayukansu sakamakon tashin wasu bama-bamai da aka dasa a gefen hanya a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na gudanar da samame a wajen sansanin yan gudun hijra na Jenin a lokacin da bam na farko ya tashi a karkashin motarsu. Lokacin da karin sojoji suka isa wajen kuma, wani bam din ya sake tashi ain da ya yi ajalin soja daya da raunata wasu da dama. Kungiyar da ke kula da fursunoni Falasdinawa ta ce sojoji sun kama mutum 28. Tun bayan soma yakin Gaza ake samun karuwar tashin hankali a Gabar Yamma da kogin Jordan gami da samame da kamen mutane da sojojin Isra'ila suke yi

Wata Sabuwa: An Halasata Yi Amfani Da Tabar Wiwi A Brazi

Image
  An Halasata Amfani Da Tabar wiwi wadda Ba Ta Wuce Ƙima Ba A Brazil Kotun ƙoli a Brazil ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da mallakar tabar wiwi, don amfanin kai. Daga yanzu wadanda aka kama da kunshin ganyen tabar ɗan kaɗan ba za su fuskanci hukuncin aikata laifi ba, amma ana yi cin su tara idan ta zarta kima. Yau Laraba ne dai kotu za ta ci gaba da zama domin yanke hukunci a kan yawan miyagun ƙwayoyi da za a ƙayyade. Alkalan kotun sun ce dole ne ya kasance akwai bambanci wajen hukunta masu amfani da kayan maye da kuma masu dillancinsu. Masu fafutuka sun ce hukuncin zai amfanar da dubban jama'a, musamman matalauta da marasa galihu a cikin al'umma, wadanda ake tuhuma da daure su a gidan yari idan aka kama su da tabar wiwi.

Wata Sabuwa: Matsanancin Zafi Yayi Sanadayar Mutuwar Mutane Da Dama A Pakistan

Image
Tsananin Zafi Na Ci Gaba Da Kashe Mutane A Pakistan Jami'an kiwon lafiya a Pakistan sun ba da rahoton ƙaruwar mace-mace sakamakon tsananin zafi inda lardin Sindh ne ya fi fuskantar bala'in zafin da har yanayin zafi ya tashi zuwa digiri arba'in da bakwai a ma'aunin salshiyos. A Karachi kuma, birni mafi girma, sama da mutum 260 ne aka kwantar a wani babban asibiti da zazzabin cizon sauro tun ranar Lahadi. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta gida ta bayar da rahoton tattara fiye da sau uku adadin gawarwakin mutanen da suka mutu sakamakon tsananin zafi a cikin ‘yan kwanakin nan. Domin a sassauta lamarin ne aka kafa cibiyoyin ba da agajin gaggawa ga jama'a. A halin da ake ciki, mazauna birnin Karachi sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da katsewar wutar lantarki da ya kawo cikas ga samun iskar fankoki da na AC da kuma tsadar wutar Lantarki.

Da Dumi-Dumi: 'Ƴan Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa A Jihar Borno

Image
Da Dumi-Dumi: 'Ƴan Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa A Jihar Borno . Wasu ‘yan ta’adda da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun yi garkuwa da wani alkalin babbar kotun ƙasa, mai shari’a Haruna Mshelia, tare da matarsa da direbansa da kuma mai tsaron su a hanyar Damaturu-Kamiya zuwa Buratai-Buni Gari a jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a hanyar Buratai-Buni-Gari a daidai lokacin da mai shari’a Mshelia ke komawa Maiduguri inda yake aiki a babbar kotu a jihar Borno. Shehun Borno Ya Bukaci Tinubu Ya Kwato Kananan Hukumomin Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno Wata majiya ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai ne suka tare motar Alkalin tare da tare hanya duk da yunkurin tserewa da ya yi, sai wasu gungun ‘yan tadar sun tare motar ta baya, daga bisani suka tasa ƙeyarsu zuwa dajin Sambisa. Rundunar ‘yansandan jihar Borno, ta bakin kakakinta, ASP Nahum Daso, ta t...

Inalillahi wa Innna Ilaihi Raji'un! Miji Da Mata Sun Rasu A Lokacin Aikin Hajji

Image
Mata Da Miji Ƴan Amurka Sun Mutu A Lokacin Aikin Hajji Wasu ma'aurata ƴan Amurka da suka mutu a lokacin aikin Hajji a Saudiyya sun shafe sama da sa'o'i biyu suna tafiya a cikin zafi kafin su mutu sakamakon tsananin zafi kamar yadda 'yarsu ta shaida wa BBC. Alhaji Alieu Dausy Wurie mai shekaru 71 da Haja Isatu Wurie mai shekaru 65 a yankin Bowie dake jihar Maryland na daga cikin kimanin mutum 1,300 da suka mutu a yayin gudanar da aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya. Tsananin zafi na bana ya wuce maki digiri 50 na ma'aunar salshiyos a wasu lokuta. Saida Wurie ta shaida wa manema labarai cewa tawagar da iyayenta suke ciki na yawon bude ido ta kasa samar musu da kayayyakin da ta yi alkawari da suka hada da abinci da isasshen ruwa. Ma’auratan ‘yan asalin ƙasar Saliyo sun bace ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni, makonni biyu da isa ƙasar Saudiyya.        Bayan kwanaki sai aka sanar da ƴarsu da cewa sun rasu. 'Yar da ke cikin makoki ta shaida wa BBC cewa aikin Hajjin na...

Wata Sabuwa: Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Yi Watsi Da Shirin Sauke Sarkin Musulmai

Image
Wata Sabuwa: Gwamnatin Jihar Sokoto Tayi Watsi Da Yin Kurin  Sauke Sarkin Musulmai . Gwamnatin jihar Sokoto ta yi watsi da rade-radin da ke cewa tana shirin tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III. A cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa, ya yi tir da kokarin kawo cikas ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da Majalisar Sarkin Musulmi. Wannan jita-jita dai ta samo asali ne daga zargin da ƙungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi da ke ikirarin cewa gwamnatin jihar na yunkurin tsige Sarkin Musulmi. Bayan haka ne mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jaddada a ranar Litinin cewa matsayin Sarkin Musulmi wata cibiya ce da ake mutuntawa da ya kamata a kiyaye kuma a kare. Da yake jawabi a wajen taro kan rashin tsaro a Najeriya da aka gudanar a jihar Katsina, Shettima ya bayyana muhimmancin rawar da Sarkin Musulmi ke takawa, inda ya bukaci mataimakin gwamnan jihar Sokoto Idris Gobir da ya kiyaye wannan matsayi d...

Yanzu-Yanzu: Shahararan kamfanin Nan "Apple" Ya Saɓa Doka A Manhajarsa -Tarayyar Turai.

Image
Da Dumi-Dumi: Kamfanin Apple Ya Saɓa Doka A Manhajarsa - Tarayyar Turai. Hukumomin Tarayyar Turai sun zargi kamfanin Apple da laifin keta sabbin dokokin da aka tsara don sarrafa manyan kamfanonin fasaha. Hukumar ta ce manhajar Apple na murƙushe kasuwannin abokan hamayya, wanda ke zama karo na farko da ya sami kamfani da ke saɓa dokar Kasuwar Dijital (DMA). Kamfanin na fuskantar yuwuwar tarar kusan kashi 10 cikin 100 na kuɗaɗen shigar sa na duniya idan ya gaza bin ka'idoji. An bai wa kamfanin Apple ɗin damar yin nazari kan sakamakon binciken farko da aka samu, kuma zai iya kaucewa cin tarar idan ya dawo da wata shawara wacce ta gamsar da Tarayyar Turai. Kamfanin yana cajin masu haɗa manhajoji kaso 30 akan manhajarsa.

Da Dumi-Dumi: Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Buharin Yadi A Kaduna

Image
Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Buharin Yadi A Kaduna. Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren satar shanu da safarar makamai, da tashe-tashen hankula a jihohin arewacin ƙasar da dama. Ha...

Inalillahi! Dan Dazon Mutanen Dake hijira Aduniya Dan Gudun Tashin Hankali kullum Ƙarawa Suke.

Image
Yawan Mutanen Da Ke Tsere Wa Tashin Hankali A Duniya Na Ƙaruwa. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa mutane miliyan 120 ne aka tilasta musu barin gidajensu saboda yaki da tashin hankali da kuma tsanantawa, wanda ke nuna adadin ya ƙaru a shakera 12 a jere. Hukumar ta ce yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya yanzu ya yi daidai da ɗaukacin al'ummar ƙasar Japan..Sabbin rikice-rikice a Sudan da Gaza sun ƙara ta'azzara munin al'amarin wanda babban jami'in hukumar, Filippo Grandi ya kira "mummunan lamari mafi girma kan halin da duniya ke ciki". Ya buƙaci gwamnatoci da su magance matsalolin da ke haifar da irin waɗannan tashe-tashen hankula a maimakon yin gaggawar gyara kamar rufe kan iyakoki, lamarin da ya ce ba zai magance matsalar ba. A maimakon haka, ya yi kira da a haɗa gwiwa a tsakanin ƙasashen duniya don nemo mafita mai dorewa. Rahoton na shekara-shekara na hukumar ya nuna cewa a Sudan, rikicin da ...

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nigeria Sun Kashe 'Yan Ta'adda Adajin Taraba

Image
Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan  Bindigar Daji A Dajin Taraba, Sun Ƙwato Makamai Da Kayan Aiki. Za A Iya Gamawa Da ‘Yan Bindiga Cikin Mako 2 Idan An Yi Niyyar Haka – Gwamna Dauda.  Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara. Dakarun Sojoji Nijeriya a runduna ta 6, sun yi nasarar fatattakar ƴan bindiga a dajin Chinkai na jihar Taraba a ranar 11 ga watan Yuni, 2024. Wannan farmakin na da nufin yaƙi da satar mutane da masu aikata laifuka a ƙaramar hukumar Wukari. Ta hanyar amfani da rahotannin sirri, Sojojin runduna ta bataliya 93 sun ƙaddamar da zurzurfan bincike a cikin dajin, wanda ya shahara wajen garkuwa da masu garkuwa da mutane. Rundunar Sojojin Kasar Sin Ta Ci Gaba Da Yin Atisayen Soja a Wuraren Dake Kewayen Tsibirin Taiwan.  Sojoji Sun Lalata Sansanin ‘Yan Ta’adda A Kaduna Da Katsina.  Sumame Sojojin ya kai ga lalata sansanoni da dama da ke da alaka da gungun masu garkuwa da mutane da kuma kwato kayayyakin aikin da ...

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Ya Fara Biyan Albashin Watan Yuni Domin Hidimar Sallah

Image
Gwamnantin Zamfara Ta Fara Biyan Albashin Watan Yuni Domin Hidimar Sallah Daga Karshe EFCC ZA Ta Gurfanar Da Yahaya Bello A Kotu. Gwamnan Sakkwato Ya Ba wa Ma’aikata Kyautar Dubu Talatin Goron Sallah  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da fara biyan sabon tsarin Albashi na Naira dubu Talatin daga dubu Shida a Yau na wannan watan da muke ciki don ma’aikata suyi hidar Sallah cikin walwala. Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a wajan taron ranar Dimokaraɗiyya a yau a filin dandalin ƴanci da ke tsakiyar garin Gusau, Babban birnin Jihar Zamfara. Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara Sin Ta Samu Nasarar Zama Mamba A Kwamitin Gwamnatocin Dake Kula Da Kiyaye Kayayyakin Al’adu Marasa Ganuwa. “A Jawabin nasa gwamna Dauda ya ɗau alwashin inganta iin daɗin ma’aikata wanda abin takaicin ne tsawon shekaru da Gwamnonin da aka yi suka shuɗe a Zamfara sun gaza biyan ma’aikata tsarin albashi mafi ƙaranci na dubu Talatin sai na dubu shida. A kan haka ne ya tabba...

Da Dumi-Dumi: Kashim Shettima Ya buƙacil Likitoci Ƙasar Su Bada Nasu Gudun mawar Wajan Inganta Nigeria

Image
Kashim Shettima,  M ataimakin Shugaban Kasa,Ya Buƙaci  Likitocin Najeriya Su Taimaka wajen Inganta Ƙasar . Bayanan hoto,Kashim Shettima ya koka kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa zuwa ƙasashen ƙetare Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau. Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka z...

Wata Sabuwa: 'Ƴan Jaridun Kano Sun Da Katar Da Kawo Rahotanni Daga Gidan Gwamnatin Kano

Image
‘ Yan Jarida Sun Dakatar Da Kawo Rahotanni Daga Fadar Gwamnatin Kano. Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da kauracewa kawo rahoto ko wasu labarai na ayyukan gwamnatin jihar Kano. Wannan na zuwa ne bayan zargin cin zarafi da rashin girmama aikin ‘yan jarida da gwamnatin jihar da jami’anta ke yi wa ‘yan jarida. Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS Yau Litinin Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Za Su Cimma Matsaya Kan Mafi Ƙarancin Albashi Ƙungiyar ta kuma soki gwamnati da mayar da kwararrun ‘yan jarida gefe tare da fifita waɗanda ba su da ƙwarewa ko kuma ƙwazo a wajen aiki. Sakamakon haka, ƙungiyar ta ke sanar da dakatar da kawo duk wani rahoto ko labarai kan abubuwan da suka faru na gwamnati ko halartar taron manema labarai, ko yin hira da jami’an gwamnatin jihar har sai an sami cikakkiyar fahimta da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kare lafiyarsu kafin mu ci gaba da aiki kamar yadda yake a ƙunshe cikin sanarwar. Shugaban kungiyar...

Yanzu-Yanzu: An Rufe Asibitin Farar Hula Na Ƙarshe A Birnin Sudan

Image
An Rufe Asibitin Farar Hula Na Ƙarshe A Birnin Sudan Likitoci a daya daga cikin asibitocin ƙarshe da ke aiki a birnin El-Fasher na Sudan da aka yi wa ƙawanya sun ce an tilasta musu rufe asibitin sakamakon harin da aka kai. Asibitin, wanda ke samun tallafin Médecins Sans Frontières (MSF), shi ne kawai wurin da ya rage inda farar hula da suka jikkata za su iya samun magani da kulawa.  Kwanaki dai rahotanni sun nuna cewa harsasai sun afkawa asibitin wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da kuma asarar rayuka. Sai dai kuma shaidun gani da ido a yanzu sun bayyana cewa mayaƙa daga cikin dakarun RSFsun mamaye wurin da asibitin yake.  Aranar Asabar ne dakarun RSF suka isa asibitin, suka buɗe wuta kuma suka yi awon gaba da magunguna da kayan aikin jinya tare da sace motar ɗaukar marasa lafiya da kai wa ma’aikatan asibitin hari. Shugaban MSF a Sudan, Maximilien Kowalski, ya shaida wa BBC Newsday cewa, "saboda hargitsin, tawagarsu ba ta iya tantance ko akwai wadanda suka mutu ko suka jikka...

Inalillahi Wa Innna Ilaihi Raji'un! Wani Manin Yaci Yarasu A Makkah Dan Nigeria Daga Jihar Kebbi

Image
Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kebbi ta sanar da rasuwar wani maniyyaci a garin Makkah na kasar Saudiyya. A sanarwar da Alhaji Ahmed Idris, babban sakataren yada labarai na Gwamnan Kebbi, ya bayyana sunan marigayin da Abubakar Abdullahi daga garin Gulma da ke karamar hukumar Argungu. Wata Hajiyar Jihar Kebbi Ta Rasu A Makkah, Shugaban NAHCON Ya Yi Ta’aziyya, Hajjin Bana: Yau Litinin Ita Ce Ranar Ƙarshe Ta Jigilar Maniyyata Zuwa Ƙasar Saudiyya. Sanarwar ta ce maniyyacin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Marigayi Abdullahi daga Jihar Kebbi shi ne maniyyaci na uku da ya rasu a kasa mai tsarki. Sanarwar ta ruwaito Gwamna Nasir Idris ya bayyana damuwarsa kan rasuwar tare da addu’ar Allah ya bai wa marigayin hutu na dindindin, ya gafarta masa. Tuni aka yi jana’izar marigayin jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada aa Masjid Al-Ihram (Ka’aba), ranar Juma’a. Labarai Masu Nasaba Yau Litinin G...

Da Dumi-Dumi: Ƙasar Amuruka Ta Fara Dauke Sojojinta Daga Jamuriya Nijer.

Image
  Amurka Ta Fara janye Sojojinta Daga Jamhuriyar Nijar Sojojin Amurka sun fara janyewa daga Nijar kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar, Tele Sahel ta rawaito. A wani biki da aka yi a Air Base 101 da ke birnin Yamai, babban hafsan sojojin Nijar, Kanal Maj Mamane Kiaou, ya sanar da cewa, sojojin Amurka 260 daga cikin kiyasin 1,100 da aka kiyasta sun janye daga ƙasar tare da tankunan kayan aiki da dama. Maj Kiaou ya bayar da tabbacin cewa Nijar za ta tabbatar da tsaron jami'an Amurka a lokacin janyewar da ake sa ran kammalawa a tsakiyar watan Satumba. Duk da janyewar, ƙasashen biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a ranar 8 ga watan Yuni, inda suka tabbatar da cewa dangantakarsu ba za ta ɓaci ba. Janyewar sojojin ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayar a ranar 16 ga watan Maris, inda ta soke yarjejeniyar da ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da aiki a kasar nan take.

Turƙashi: Ƙungiyar ƙwadago Zata Dau Mataki Idan Har Dai Ba Ta Samu Biyan Buƙata Ba.

Image
Wane Matakin Ƙungiyar ƙwadago Za Ta Ɗauka Idan Ba Ta Samu Biyan Buƙata Ba? A ranar Litinin ɗin nan ne ake sa ran kammala tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago, yayin da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC ke jiran matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka kan batun biyan mafi ƙarancin albashi na N250,000. A ranar Juma’ar da ta gabata ne kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kammala taronsa, inda gwamnatin tarayya da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka cimma matsaya kan kuɗirin naira 62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata. A halin da ake ciki dai a yanzu, ƙungiyayin ƙwadagon biyu sun dage a kan biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata na naira 250,000. Sai dai kungiyar gwamnonin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa duk wani mafi ƙarancin albashi da ya haura N60,000 ba zai ɗore ba. Illar da yajin aiki ke yi wa ƙasa4 Yuni 2024 Yadda ƴan ƙwadago suka ts...

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Jihar Kano Ta Biya Ma Ɗalibai Kudin Jarabawa Sama Da 119,903 NECO Da NBAIS

Image
Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan ₦2,910,682,780 don biyawa ɗalibai 119,903 kuɗin jarrabawar NECO da NBAIS ta shekara 2024. Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a Kano, inda yace duk wani ɗalibi da ya samu darussa hudu daga cikin darussan da ya rubuta Jarrabawar samun cancatar zana Jarrabawa a jihar zai amfana da shirin biyan kudin jarabawar na gwamnatin Kano, sannan za a yi masa rijistar zama don zana Jarrabawar. Rikicin Sarautar Kano: Kallo Ya Sake Komawa Kotu Ƙungiyar Likitocin Kano Za Ta Tsunduma Yajin Aiki Doguwa ya kara da cewa, Gwamnati za ta biyawa kowane ɗalibi ₦24,250 da kuma dubu ₦21,000 don zana Jarrabawar NECO da NBAIS, tare da bayanin cewa Gwamna ya yi fatali da shawara biyawa kowane ɗalibai kuɗin jarrabawar sai wanda ya lashe darussa hudu a kowane darasi.  Ya bukaci iyaye da ka da su dakatar da yaransu ...

Yanzu-Yanzu: Sojojin Isra'il Sun Yi Nasarar Ceto Mutum 4 Daga Cikin Waɗanda A Kayi Garkuwa Da Su.

Image
  Sojin Isra'ila Sun Ce Sun Ceto Mutum 4 Cikin Waɗanda Da Hamas Ta Yi Garkuwa Da Su. Dakarun Isra'ila sun ce sun ceto ceto mutum huɗu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin wani samame da suka kai Nuseirat a tsakiyar Gaza. Mutanen sun hada da Noa Argamani da Almog Meir Jan da Andrey Kozlov da kuma Shlomi Ziv. Rundunar sojin Isra'ila ta ce mutanen suna cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoban bara, kuma ta tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.  Rahotanni sun ce Firaiminista Benjamin Netanyahu ya zanta ta waya da ɗaya daga cikin mutanen da aka ceto mai suna Noa Argamani. Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kashe mutane aƙalla 50, ciki harda da ƙananan yara a lokacin samamen .

Da Dumi-Dumi: "Mun Musa Cimma Matsayia Akan Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata" Gwamna Uzodimmo

Image
"Mun kusa Cimma Matsayia Akan Sabon Tsarin Albashin Ma'aikata". Gwamna uzodimmo. Gwamnan jihar Imo State, Hope Uzodimma, ya ce kwamitin tsara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kusa cimma matsaya a kan sabon albashin. A ƙarshen taron kwamitin, gwamna Uzodimma, ya ce bayan shafe sa'oi 12 ana tattaunawa tsakanin mabobin kwamitin, an cimma matsaya kan shawarar da ta dace su bai wa gwamnati. Gidan talabijin ɗin Channels ya ruwaito gwamna Uzodimma, ya na cewa: “Mun yi tattauwa mai daɗin gaske kuma ana iya cewa mun cimma matsaya a matakinmu na ƙaramin kwamitim, don haka idan muka je ga babban kwamiti komai zai tafi lafiya.” Ya yi bayanin cewa kwamitin ya tuntuɓi duk waɗanda ya kamata, kuma sakamakon rahoton zai zamo abin da ake sa ran yin amfani da shi wajen cimma matsaya a babban kwamitin da zai yi aiki na gaba a kan sabon albashin. Gamayyar kungiyoyin ƙwadago a Najeriya dai ta ƙi amincewa da tayin naira 60,0000 da gwamnati ta yi mata a matsayin mafi ƙaranci...

Inalillahi! An kashe Mutane Sama Da 120 A Kauyen Sudan, Lamarin Ya Tada Hankalin Duniya

Image
Kisan Mutum 150 A wani Ƙauyen Sudan Ya Tayar Da Hankalin Duniya. Aƙalla mutum 150 ne ake tunanin an kashe a kisan kiyashin da aka yi a wani ƙauye da ke tsakiyar ƙasar Sudan, wanda ake zargin mayaƙan ƴan tawaye na RSF da aikatawa. Yanzu sama da shekara ɗaya ke nan mayaƙan ƙungiyar RSF na yaƙi da dakarun gwamnati a wani yunƙuri na ƙwace iko da ƙasar. Har yanzu RSF ba ta ce uffan ba game da zargin da ake yi mata na kisan mazauna ƙauyen, sai dai a jiya Alhamis ƙungiyar ta bugi ƙirjin cewa ta kai hare-hare kan wasu cibiyoyin dakarun sojin gwamnati guda biyu..Bidiyon da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta bayan harin na ranar Laraba ya nuna yadda aka shirya gawawwaki bila-adadin waɗanda za a yi wa jana'iza a garin Wad al-Nourah da ke jihar Gezira. Wani mai fafatuka - ɗan wata ƙungiya mai rajin ganin ƙasar ta koma kan tafarkin mulkin dimokuradiyya ne ya naɗi bidiyon. Ƙungiyar masu fafutikar ta Madani Resistance Committe ta ce a yanzu "tana jiran samun jimillar mutanen da aka kashe d...

Yanzu-Yanzu: Ministan Kudi Wale Edu, Ya Miƙa wa Shugaban Kasa Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashi

Image
Da Dumi-Dumi: Edun Ya Mika Wa Tinubu Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata Biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaban sabon tsarin mafi karancin albashin. Sanarwar na zuwa ne kwanaki biyu bayan Tinubu ya bayar da umarnin gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi da kuma nazarin abin da ke tattare da shi. Hajjin Bana: NDLEA Ta Kama Maniyyata Dauke da Hodar Iblis A Legas. Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Ci Gaba Da Biyan Tallafin Man Fetur. Rahoton na ministan kudi an ce zai zayyana wasu sabbin matakan mafi karancin albashi tare da tasirin kasafin ga gwamnatin tarayya. Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a Litinin, domin neman karin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati. A gefe guda kuma ma’aikatan na bukatar janye karin kudin wutan lantarki da aka yi a baya-bayan nan. Labarai Masu Nasaba An Tsaurara Tsaro Bayan Fara Shari’a Kan Rikicin Masarautar Kano Fadar Shu...

Wata Sabuwa: Hukumar NDLEA Ta Kama Wasu Maniyyta Da Hodar Iblis

Image
Hukumar NDLEA Ta kama Maniyyata Da Hodar Ibilis A Legas Jami’an hukumar yaƙi da masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, sun kama wasu maniyyata da ke shirin zuwa aikin hajji da hodar ibilis a wani sumame da suka kai a otal din Emerald da ke Ladipo a jihar Legas, jiya Laraba. Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi ne ya tabbatar da kamen. Waɗanda aka kama sun haɗa da wani Usman Kamorudeen da Olasunkanmi Owolabi da Fatai Yekini, da kuma wata mata, Ayinla Kemi. Jami’an hukumar ta NDLEA sun gano kwalayen hodar iblis 200 kowannensu nauyinsa ya kai kilogiram 2.20, waɗanda ake zargin za su haɗiye kafin su tashi zuwa ƙasa mai tsarki. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yaba wa jami'an hukumar bisa nasarar da suka samu ta cafke mutanen. Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da bin diddigi tare da kamo mutanen da ke yunƙurin amfani da addini wajen aikata miyagun laifuka. Marwa ya bayyana muhimmancin kare martabar ƙasar daga iri...

Da Dumi-Dumi: Anyi Nasarar Ceto Baƙin Haure Sama Da 80 A Cikin Ruwan Birtaniya

Image
An Ceto Baƙin Haure 80 Ciki Har Da Yara Daga Ruwa A Birtaniya Kimanin baƙin haure 80 da suka hada da aƙalla yara uku ne aka ceto bayan da jirgin ruwansu ya samu matsala wajen tsallaka tekun Birtaniya. An tura jiragen ruwa na Dover da Walmer don taimaka wa jami'an tsaron kan iyaka bayan rahotannin da aka samu na mutane da dama a cikin ruwa kimanin mil 10 daga gabar tekun Kent a safiyar Alhamis. Aikin ceton da hukumomin Birtaniyya ke jagoranta, ya haɗa da jiragen ruwa biyu na jami'an tsaron kan iyaka, da jiragen ceto guda biyu, da na Faransa guda biyu, da kuma wani jirgi mai sauƙar ungulu na masu tsaron gaɓar teku. Ana kyautata zaton jirgin ruwan ya isa tekun Birtaniya ne bayan da wani jirgin ruwan Faransa ya lulluɓe shi kafin ya shiga halin tsaka-mai-wuya. Ana tunanin wasu baƙin haure sun koma cikin tekun Faransa, kuma ana iya kawo waɗanda jiragen ruwa na Birtaniya suka ceto zuwa Dover. A watan da ya gabata, alƙaluman ma’aikatar cikin gida ta Bitaniya sun nuna cewa sama da baƙin...

Yanzu-Yanzu: A Yau Ne Ake Gudanar Da shari'a Masarautar Kano.

Image
Yau Ake Gudanar Da Shari'a Kan Masarautar Kano A yau Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Kano za ta fara zaman sauraron ƙarar da Aminu Babba Ɗan'agundi ya shigar gabanta inda yake ƙalubalantar matakin majalisar dokokin jihar ta Kano na rushe masarautu biyar, tare da cire Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin kano, da mayar da Muhammadu Sanusi II, a kan sarautar. Dambarwar sarautar ta kai ga Muhammadu Sanusi na biyu, wanda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya mayar a kan karaga yake zama a gidan sarkin, tare da zama a fadar da ke ƙofar kudu, yayin da shi ma Aminu Ado Bayero ke zama a gidan sarki da ke unguwar Nassarawa. Al'ummar Najeriya da dama musamman na jihar ta Kano sun zuba ido don ganin yadda za ta kaya ganin yadda mutanen biyu ke ja-ni-in-ja-ka kan masarautar Kanon mai ɗinbim tarihi. An jibge jami'an tsaro a hanyoyin zuwa babbar kotun, inda ake sa ran Mai Shari'a Abdullah Muhammad Liman zai fara sauraron ɓangarorin da ke cikin wannan ƙara.

Wata Sabuwa: Za A Fara Biyan Musu Ajiyan Banki Heritage Kuɗinsu Cikin Sati Guda NDLC

Image
Za mu fara biyan masu Ajiya A Bankin Heritage Kuɗinsu Cikin Mako Ɗaya - NDIC. Hukumar kula da harkokin bankuna a Najeriya ta NDIC ta ce za ta fara biyan masu ajiyar kuɗi a Bankin Heritage kuɗaɗensu cikin kwana bakwai. Shugaban hukumar, Bello Hassan, ya faɗa a yau Laraba yayin taron manema labarai cewa doka ta ƙayyade kwana 30 a matsayin wa'adin da za su biya kwastomomi kuɗinsu. A ranar Litinin ne Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da sanarwar ƙwace lasisin bankin saboda abin da ya kira "gazawa wajen inganta harkokin kuɗinsa". "Binciken farko-farko ya nuna kuɗaɗen ajiyar mutane sun kai naira biliyan 650 yayin da bankin ya ba da bashin biliyan 700," in ji Bello. Ya ƙara da cewa daga cikin mutum miliyan 2.3 da suka ajiye kuɗi a bankin, kashi 99 cikin 100 ne suka ajiye ƙasa da naira miliyan biyar, wanda shi ne mafi yawan adadin da NDIC ke ba da inshora a kai.

Yanzu-Yanzu: An Kama Ministan Wasanni Na Africa Ta Kudu Bisa Wasu Dalilai.

Image
An kama Ministan wasanni Da Zargin Cin Hanci A Afirka Ta Kudu An kama Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu, Zizi Kodwa, bisa zargin cinhanci da rashawa. Ana kyautata zaton zai fuskanci tuhuma a gaban kotu da ta shafi karɓar kuɗi kusan dala 85,000 don nuna tasirinsa wajen ba da kwangilar wasu ayyukan gwamnati. Wani rahoton hukuma ne ya ambaci sunansa bayan ya binciki zarge-zarge kan wasu kamfanoni da mutane game da yadda gwamnati ta mamaye wasu harkoki. Sai dai Mista Kodwa ya musanta duka zarge-zargen. Mintuna 55 da suka wuceAn ƙirƙiro fasahar da matasa za su ga yadda za su zama idan sun girma, Bayanan hoto,Mutum zai riƙa magana da mutum-mutumin da aka yi mai ƙwaƙwalwa kamar shi. Masana a jami'ar kimiyya da fasaha ta Massachusetts (Massachusetts Institute of Technology ) da ke Amurka, sun ƙirƙiro wata fasaha da za ta bayar da dama ga masu amfani da ita su iya yin magana da ƙirƙirarran mutum mai kamanninsu ta komai da ke zaman kamarsu idan sun girma. Wanan fasaha da aka yi wa laƙabi da...

Da Dumi-Dumi: Bababar Ƙungiyar Kwallan Kafa, Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Koc

Image
Babbar Ƙungiyar Wasn Kwallan Kafa,Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta sanar da nada Antonio Conte a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta a yau Laraba. Conte ya kulla yarjejeniya da kungiyar da ke buga gasar Seria A har zuwa karshen watan Yunin 2027. Tinubu Ya Bai Wa Minista Wa’adin Kwana 2 Don Samar Da Tsarin Mafi Ƙarancin Albashi Neja: An Ceto Mutane 7 Da Suka Makale Wajen Hakar Ma’adanai Shugaban kungiyar Aurelio De Laurentiis, ya nuna jin dadinsa kan daukar Conte. Ya ce Conte hazikin mai horaswa ne kuma ya aminta da irin tarihin da ya kafa a baya, shi ya sa ya amince wajen daukarsa. Conte ya taba horas da kungiyoyin Chelsea, Tottenham da Juventus a baya. Labarai Masu Nasaba Rashin Osimhen A Cikin Tawagar Nijeriya Babbar Asarace – Samson Siasia. Champions League: Real Madrid Ta Zama Zakara Bayan Doke Dortmund. A nasa bangaren, Conte ya ce Napoli babbar kungiya ce wadda yake da yakinin za su kafa wani tarihi tare.

Yanzu-Yanzu: Al'ummar Garin Neje Na Ƙoƙarin Zaƙulo Mutanen Da Kasa Ta Danne

Image
Ana Ƙoƙarin Zaƙulo Mutane 30 Da Ƙasa Ta Rufta Da Su A Neja Mutum 30 ne ƙasa ta danne bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da aka ceto mutum shida waɗanda suka samu raunuka. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, kuma ana ganin cewa mamakon ruwan sama da aka samu ne ya haifar da lamarin. Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa BBC a safiyar yau Laraba cewa ana wani yunƙuri na samar da iskar shaƙa ga mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin ƙasa. Neja na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke ƙunshe da albarkatun ƙasa masu yawa, wadda kuma ke fama da matsalar tsaro. A irin waɗannan yankuna akan samu wuraren haƙar ma'adanai da ke aiki ba bisa ƙa'ida ba kuma ba a ɗaukan matakan kariya da suka kamata. Mintuna 29 da suka wuceMun ɗauki aniyar rage talauci da kashi 10 duk s...

Da Dumi-Dumi: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Bai Wa Minista Wa'adin Samar Da Tsarin Mafi Karancin Albashi

Image
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Ya Bai Wa Minista Wa’adin Nan Da 'Yan Kwanaki kadan Ya Samar Da Tsarin Mafi Ƙarancin Albashi. Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci . Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun wa’adin sa’oi 48 domin gabatar masa da sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata zai ci domin nazari da kuma daukar mataki a kai. Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya sanar da umarnin bayan wata ganawar da shugaba Tinubu ya yi da kwamitin da ke tattaunawa da NLC, jim kadan bayan dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Litinin. Saurayi Da Budurwarsa Sun Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa A Kano ‘Yan ta’adda 176 Sun Mika Wuya, An Cafke 57 A Tafkin Chadi – MNJTF Idris, ya bayyana cewar bangarorin biyu, wato na gwamnati da kuma shugabannin kwadago za su ci gaba da ganawa a tsakaninsu domin cimma yarjejeniya a kan sabon tsarin mafi karancin albashin cikin mako guda. Ministan, ya ce daga ciki...

Da Dumi-Dumi: Gwamna Dauda Lawal Yajaddada Da Cewa Na Tsaro Rayukan Al'ummar Zamfara

Image
Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Ƙudirinsa Na Tsaron Rayukan Al’ummar Zamfara. A faɗi-tashin da yake yi wajen samar da ingataccen tsaro, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Zamfara. A ranar Talatar nan ne gwamnan ya halarci bikin yaye wasu dakaru na musamman, waɗanda ke ƙarƙarshin Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ake kira ‘Agro Rangers’ a Jihar Zamfara. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, dakarun na ‘Agro Rangers’, jami’ai ne na musamman a Hukumar ta Sibil Difens, waɗanda suka samu horo mai zurfi. Ya kuma ƙara da cewa, an horar da jami’an na musamman a shirye-shiryen gudanar da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ’yan bindiga a Jihar Zamfara. Labarai Masu Nasaba Hadin Gwiwa Da Sin Ya Ba Matasan Kasashen Afirka Karin Damammakin Raya Kai ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Bindiga 4 A Kaduna  A yayin jawabinsa a wajen bikin, gwamna Lawal ya yaba wa huku...