Posts

Showing posts from January, 2025

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Zata Fara Biyan 'Ƴan Bautan Kasa(NYSC) 77'000

Image
' Za Mu Fara Biyan 'Ƴan NYSC Alawus Din 77,000 Daga Wata Febrairu'. Shugaban hukumar kula da matasa masu yiwa ƙasa hidima NYSC, Birgadier Janar Yushau Ahmed ya ce za a fara biyan matasan alawus din naira 77,000 daga watan Fabrairun 2025. Shugaban hukumar ya faɗi hakan ne a jihar Katsina a lokacin da yake yi wa sabbin matasan da aka ɗauka na rukunin 'C' jawabi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Yushau ya tabbatar da cewa ƙarin alawus ɗin na cikin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 kuma zai fara aiki ne da zarar an amince da kasafin kuɗin. "Wannan watan na Janairu ya riga ya ƙare, amma da zarar an amince da kasafin kuɗin a watan Fabrairu mai kamawa, za ku fara karɓar naira 77,000 a maimakon 33,000 da ake biya yanzu,'' in ji shi. Ya kuma tabbatar wa matasan cewa ba za a aika su yankunan da babu tsaro ba. A ranar 25 ga watan Satumban bara ne dai gwamnatin ƙasar ta sanar da yi wa ƴan bautar ƙasa ƙari a alawus ɗin su zuwa naira 77,000 da zai soma aiki d...

Inalillahi! Motar Mai Ta Fashe A Jihar Jigaw

Image
'Ƴan Sandan Jihar Jigawa Sun Tabbatar Da Fashewar Tankar Mai A Dutse. Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta tabbatar da fashewar tankar mai a wani gidan mai da ke Dutse, babban birnin jihar a daren jiya Alhamis. A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar SP Lawan Shiius Adam ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba a haɗarin. Ya ce tankar ta fashe ne da misalin ƙarfe 7 na dare a gidan man Shakkato da ke kan titin Kiyawa a Dutse a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juye man cikin tankin ƙarƙashin ƙasa. Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce bayan samun labarin afkuwar lamarin, tawagar ƴan sandan yankin tare da masu kashe gobara suka yi gaggawar isa wurin inda aka yi nasarar kashe gobarar. Fashewar tankar mai dai ba sabon abu bane a ƙasar baki ɗaya, inda ko a watan Janairun nan kaɗai an samu fashewar tankar mai aƙalla sau uku, wanda ya janyo asarar rayuka fiye da 80. Ko a bara ma wata tankar mai ta faɗi a jihar ta Jigawa abin da ya kai ga mutuwar mutane 181.

Turkashi: Gaskiyar Magana Akan Seaman Abbas Ya Saki Matarsa(Hussaina)

Image
Namiji Ba Dan Goyo Bane": Da Gaske Seaman Abbas Ya Saki Matarsa Hussaina? Seaman Abbas Haruna ya karyata rade-radin cewa ya saki matarsa Hussaina, yana mai cewa suna tare cikin soyayya da zaman lafiya.  Ya kuma tabbatar da cewa matarsa ta kwanta asibiti har tsawon kwanaki 10 amma yanzu ta warke kuma tana shirin komawa gida Abbas ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Hussaina kan kudin tallafi, yana zargin wasu ne ke kokarin haddasa rudani a tsakaninsu. Gombe - Seaman Abbas Haruna, sojan ruwan Najeriya da aka sallama daga aiki ya yi magana kan rade-radin da ake yadawa cewa ya saki matarsa Hussaina.  A cikin wani bidiyonsa da ke yawo a kafofin sada zumunta, Seaman Abbas ya warware rudanin da aka samu game da zamantewarsa da Hussaina.

Yanzu-Ynazu: An Gano Akwatin Da Yake Daukar Bayanai Na Jirgin Saman Da Yayi Hatsarin

Image
An Gano Bakin Akwatin Da ke Nadar Bayanai Na Jirgin Saman Amurka Da Yayi Hatsari. An gano baƙin akwatin da ke naɗar bayanan abubuwan da suka faru a lokacin da jirgin fasinjan Amurka ya yi haɗari. Yanzu haka jami'ai sun dukufa domin gano abin da ya janyo jirgin ya yi taho mu-gama da wani jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a yayin da ya ke ƙokarin sauka. Baƙin akwatin zai taimaka wajen gano abin da ya faru a lokacin haɗarin da kuma sauƙaƙawa masu bincike aikinsu. An yi amanna mutum 67 da ke cikin jiragen biyu sun mutu.H iragen sun yi taho mu-gama ne yayin da suke dab da sauka a filin jirgin saman Reagan da ke Washington DC. Mahukunta a Amurka sun ce za a kammala tattara dukkan bayanan da suka dace a game da haɗarin jiragen a cikin kwanaki 30. Sai dai Shugaba Trump ya ɗora alhakin haɗarin kan rikon sakainar kashi da gwamnatin Biden da ta wuce ta yi a fannin sufua sa ya lalace.

Innalillahi! Wani Mahaifi Ya Kashe 'Yarsa Saboda TikTok.

Image
Mahaifi Ya kashe ƴarsa Saboda Bidiyon Da Take Yi A TikTok. Wani mahaifi da ya mayar da iyalinsa Pakistan daga Amurka ya tabbatar da kashe ƴarsa bayan ya hana ta bidiyo a TikTok, kamar yadda ƴansanda suka bayyana. An gurfanar da Anwar ul-Haq ne bisa zargin kashe kai bayan ya tabbatar da kashe ƴarsa ɗin mai suna Hira a kudu maso yammacin birnin Quetta a ranar. Da farko ya bayyana wa masu bincike cewa wasu ƴanbindiga ne suka kashe ta. Mahaifin, wanda yake da shaidar zama ɗan Amurka, ya ce ya gano bidiyoyin da ƴarsa ke saki ba su dace ba. Ƴansanda sun ce suna duba yiwuwar mayar da kisar a matsayin kisar wadda ta ɓata wa danginta suna da ake kira 'humanity killing', lamarin da ba sabon abu ne a Pakistan, musamman a kan mata. Ɗaruruwan mutane - musamman mata- ake kashewa duk shekara a irin wannan kisan a Pakistan, kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙi ɗan'adam suka nuna. Yawanci ƴan'uwa ne suke kashe wadda suke ganin ta jawo wa danginsu abin kunya. A game da Hira Anwar, wadda tak...

Yanzu-Ynazu: Israela Ta Kashe Fasdinawa Goma(10)

Image
Ma'aikatar Lafiyar Hamas Tace Isra'ila Ta Kashe Falasɗinawa 10. Ma'aikatar lafiya a Falasɗinu ta ce hari ta sama da Isra'ila ta kai yamma da gaɓar kogin Jordan da ta mamaye ya hallaka aƙalla Falasɗinawa 10. An kai harin ne a yankunan Tunbas da Samaria da ke arewacin kogin Jordan. Wakilin BBC ya ce ƴan makonnin nan Isra'ila ta zafafa kai hare-haren soji a arewacin yamma da gaɓar Kogin Jordan musamman a Jenin, inda hukumomin Falasɗinu suka gwabza faɗa da Hamas da mayaƙan jihadi. Hotunan bidiyo da ake kyautata zaton a garin Tamoun ne, ya nuna yadda mutane suka cika maƙil gaban wasu gine-gine da ya lalace domin zaƙulo waɗanda suka tsira da rai.

DA Dumi-Dumi: NlC Zata Yi Zanga-Zanga Adawa Akan Karin Kudin Kira.

Image
NLC Zata Yi Zanga-Zanga Don Adawa Da ƙarin kuɗin kiran Waya.  Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Febrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da shi. Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba. NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin kakabawa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi. Ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito. Ta kuma yi kira ga ma'aikata da kuma ɗaukacin ƴan Najeriya da su tsaya kai da fata wajen yin watsi da wannan tsari da kuma waɗanda ba su a...

Yanzu-Ynazu: Tinubu Yayi Shirin Yima 'Yan Nigeria Aiki.

Image
Gwamnatin Tinubu Ta Samo Rancen Sama Da N1bn Don Tsame Najeriya Daga Duhu. Bankin AfDB zai ba da Dala miliyan 200 domin aiwatar da shirin wutar lantarki na Najeriya, wanda zai baiwa mutane 500,000 hasken lantarki. Wannan ya na daga cikin Dala biliyan 1.1 da Najeriya ta karba domin aiwatar da ayyukan samar wa 'yan kasa hasken wutar lantarki zuwa 2026 Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na ganin wannan makudan kudi da ya ke karbo wa za su taimaka wajen raba Najeriya da duhu.  Abuja - Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar da samun bashin Dala biliyan 1.1 daga Bankin Raya Afrika (AfDB) domin gudanar da aikin samar da hasken wutar lantarki a kasar. Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana hakan, ya ce ana sa ran samar da hasken wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen shekarar 2026. 

Turkashi! kujerar Shugaba Tunibu Ta Fara Rawa

Image
Matasa Sun Ajiye Tinubu, Sun Fara Kiran Rahama Sadau Ta Fito Takarar Shugabar Kasa. Wani matashi ya bukaci 'yar wasar fim, Rahama Sadau ta fito takarar shugabar Najeriya a 2027 domin shahararta da tarin masoya Wasu sun goyi bayan wannan kiran yayin da wasu suka nuna ko kusa ba ta cancaci neman kujerar Shugaba Bola Tinubu ba. Wannan na zuwa ne yayin da Rahama ta wallafa "Salaam" a soshiyal midiya, wanda ya sa mutane sama da 2,200 suka yi martani Kaduna - Soshiyal midiya ta dauki zafi da wani matashi ya nemi fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta fito takarar shugabar Najeriya a 2027.  An nemi Rahama Sadau ta gwabza da Shugaba Bola Tinubu a 2027 ne yayin da jarumar ta wallafa wani sako da ya ja hankalin dubunnan mutane.

Inalillahi!!!m Hatsarin Jirgin Sama Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Da Dama

Image
Murum 20 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Sama A Sudan Ta Kudu. Aƙalla mutane 20 ne aka tabbatar sun mutu bayan wani haɗarin jirgin sama a jihar Unity da ke Sudan ta Kudu. A cewar wani rahoton gidan radio Mir Station Mutane tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, jirgin ya yi haɗarin ne bayan ya tashi daga watae ijiyar mai a Unity a hanyarsa ta zuwa babban birnin ƙasar Juba. Fasinjoji 21 da ma'aikatan jirgin ne ke ciki a lokacin da yayi haɗarin. Rahotannin sun tabbatar da cewa matuƙin jirgin saman ya mutu, yayin da wanda ke raye a cikinsu ke cikin mayuwacin hali.

Turkashi! Koriya Tace Baza Ta Bar Ƙera Makaman Nukiliya Ba

Image
Baza Mu Daina Ƙera Makaman Nukiliya Ba - Kim Jong Un.   Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran ƙasar ta rawaito Mr Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matuƙar muhimmanci a tsarin da ƙasar ke yi na ƙarfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk ƙasashen da suka nemi tsoma baki a harkar ƙasarsa. Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama aiki. A ɓangare guda kuma Mr Trump ya ce zai sabunta hulɗar da ke tsakaninsa da shugaban na Koriya ta Arewa.

Innalillahi: Ɗaruruwan Mutane Sun Raunata A Wani Mummunan Hari

Image
Asibitoci Sun Ci ka Da  Ɗaruruwan Waɗanda Suka Samu Raunuka A Goma. Majalisar Dinkin Duniya ta ce asibitoci sun cika maƙil da 'daruruwan majinyata da suka samu raunuka a gabashin Goma, inda ƴan tawayen M23 da Ruwanda ke goyon baya suke yunƙurin ƙwace birnin daga sojojin Congo. Akwai gawarwaki da dama kan tituna ya yinda ake ci gaba da fafata yaƙi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu rahotannin yadda mayaƙan suka aikata fyade. Dr Adelheid Marschang babbar jami'ar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce WHO ta damu musamman da lafiya da tsaron mata da ƴan mata da masu juna biyu wadanda ke cikin hatsari, dama akwai yawaitar mutuwar masu juna biyu ya yin haihuwa tun kafin ɓallewar rikicin. Hukumar Lafiya ta Duniya na aiki tare da hukumomi da abokan hulda don neman mafita.

Yanzu-Ynazu: Falasdiwa Kusan Miliyan Daya Ne Suka Koma

Image
Falasɗinawa Akalla  Dari Biyar  miliyan ne Zasu Koma Gida A Yau Talata. Ana sa ran cewa Falasɗinawa sama da rabin miliyan za su koma gidajensu a arewacin Gaza a yau Talata. Ƙungiyar Hamas ta ce sama da Falasɗinawa dubu 300 waɗanda yaƙi ya tarwatsa sun koma gidajensu da aka yi raga-raga da su a arewacin Gaza a ranar Litinin. Hotunan da aka gani a yau sun nuna yadda Falasɗinawan ke tafiya a cikin motoci suna ratsa yankunan da aka yi wa rugu-rugu, sannan har yanzu akwai waɗanda suke taka sayyada a ƙoƙarinsu na komawa gida. Ƙungiyar Islamic Jihad ta saki bidiyon da ke nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda za a saki, Abel Yehud, na nan a raye, wadda ake taƙaddama kan sakin ta tsakanin ɓangarorin biyu. Isra’ila ta ce ta tabbatar cewa takwas daga cikin waɗanda aka tsara cewa Hamas za ta saki ƙarƙashin yarjejeinyar tsagaita wuta, sun mutu.

Da Dumi-Dumi: Gaskiya Magana Akan Kama Bello Turji

Image
Shin Da Gaske An Cafke Dan Ta'adda, Bello Turji? An Samu Karin Bayani kan Rade Radin A Yau Talata, Janairu 28, 2025 at 6:38 A n yada wasu rahotanni cewa rundunar sojojin Nigeriya ta yi nasarar cafke rikakken dan ta'adda, Bello Turji Labarin da ke yawo cewa sojojin Operation Fasan Yanma sun kama Bello Turji ba gaskiya ba ne.  kumayaqara da cewa babu hujjar da ta tabbatar da hakan Sautin murya da aka ce mutane biyu suna ikirarin kama Bello Turji babu gaskiya a ciki kuma yaudara ce maras tushe ko sahihanci. Wasu rahotanni sun tabbatar Bello Turji na nan a boye, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin gano inda yake domin damke sh. Gusau, Zamfara - A yan kwanakin nan rundunar sojojin Nigeriya ta matsa wurin kokarin kakkabe yan bindiga a Arewacin kasar.  Wasu sun yi ta yada labari a kafofin sadarwa cewa an cafke shugaban yan bindiga, Bello Turji a jihar Zamfara.

Alhamdulillah! Falasdinawa Suna Ta Komawa Gaza

Image
Komawar Falasɗinawa Gaza Babbar Nasara ce - Hamas. Falasɗinawa na komawa gidajensu da ke arewacin Gaza. Hamas ta ce komawar Falasɗinawa zuwa arewacin Gaza babbar nasara ce ga masu yunkurin ɗaiɗaita ƴan yankin. "Komawar waɗanda aka ɗaiɗaita babbar nasara ce ga al'ummar mu da kuma ya nuna kasawa ko shan kaye ga masu shirin ɗaiɗaita da kuma mamaye yankin," in ji ƙungiyar yayin da aka buɗe mashigar komawa a yau. Takwarar Hamas, Islamic Jihad, ta kira hakan da "martani ga dukkan waɗanda suka yi shirin ɗaiɗaita al'ummar mu". A ranar Lahadi da daddare a Isra'ila, Firaminista Netenyahu ya ce buɗe mashigar na zuwa ne bayan da Hamas ta sauka daga matsayinta kan sakin Arbel Yehud wadda ta kasance cikin ƴan ƙasar da aka yi garkuwa da su. "Hamas ta yi amai ta lashe kuma za ta cigaba da sakin ƙarin waɗanda ta yi garkuwa da su a Alhamis ɗin nan, 30 ga watan Janairu," kamar ofishin Netanyahu ya bayyana a shafin X

Yanzu-Ynazu: Isra'ila Ta Saki Falasdiwan Da Tayi Garkuwa Dasu

Image
Hotunan Murnar komawar Falasɗinawan Da Isra'ila Ta saki. Yayin da hukumomin Isra'ila suka tabbatar da sakin fursunonin Falasɗinawa 200 a yau, tuni wasu daga cikinsu suka koma gida wajen iyalansu. Za a bai wa kusan rabin mutanen damar komawa gidajensu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. Fursunoni saba'in - waɗanda aka samu da manyan laifuka - za a fitar da su zuwa maƙwbatan ƙasashe kamar Qatar da Turkiyya, yayin da za a aika wasu ƙalilan daga cikinsu zuwa Gaza. Kusan fursunoni Falasɗinawa 121 da aka saki a makon nan na zaman hukuncin ɗaurin rai da rai ne. Ga hotunan wasu Falasdinawa a yayain da suka hadu da iyalansu.

Yanzu-Ynazu: An Naɗa Gabduje Shugaban Kwamitin Gudanarwa Na FAAN

Image
Tinubu Ya Naɗa Ganduje Shugaban kwamitin Gudanarwa Na FAAN. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban jam'iyar APC, Abdullahi Umar Ganuje a matsayin shugaban hukumar gudanarwar sufurin jiragen sama, FAAN. Tinubu ya kuma naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna a matsayin shugaban hukumar bankin bayar da rancen sayen gida, wato Morgage bank. Haka kuma shugaban ya naɗa sakataren jam'iyar APC na ƙasa, Sanata Bashiru Ajibola a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NSDC. Mai magana ba shugaban ƙsar shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya sanar da naɗe-naɗen a cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Juma'a. "Shugaban Tinubu ya naɗa shugabannin hukumar gudanarwa 42 na ma'aikatun gwamnatin tarayya da sakataren hukumar gudanarwa na gidajen yari da hukumar shigi da fici da kuma ta hukumar tsaro da kai dauki ta Civil Defence," Cewar sanarwar. Sannan shugaban ya naɗa kanen ministan ayy...

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Lakurawa A Matsayin 'Ƴan Ta'adda.

Image
Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Lakurawa  A Matsayin 'Ƴan Ta'adda . Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyuka tare da ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ta ƴanta'adda. Lakurawa ƙungiya ce ta ƴanbindiga da sunanta ya yi amo a bara, duk da cewa mazauna yankunan Sokoto da Zamfara da Kebbi da suke maƙwabtaka da Nijar sun ce sun daɗe suna shigowa jefi-jefi. A takardar ƙara da gwamnatin ta shigar a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta zargi ƴan ƙungiyar da aikata ayyukan ta'addanci da sata da garkuwa da mutane da kai hare-hare kan jami'an tsaro da ma'aikatan gwamnati. Ta kuma zargi ƴan ƙungiyar da gurɓata tunanin mutane, ta hanyar ba su shawarar yi gwamnati bore. Ministan shari'ar Najeriya, Leteef Fagbeni ya ce ƴan ƙungiyar na barazana ga tsaron Najeriya, wanda hakan ya sa suka buƙaci kotu ta haramta ayyukanta, tare da ayyana ta a matsayin ta ƴanta'adda. Da yake yanke hukunci, Mai shari'a James Omotosho, ya haramta ayyukan ƙungiyar sannan ya ...

Yanzu-Ynazu: Rikici Ya Barke Tsakanin Boko Haram Da Dogo Gide

Image
Dogo Gide Ya Gwabza Fada da Mayakan Boko Haram. An sheke 'Yan Ta'adda Masu Yawa  A Yau Alhamis, Janairu 23, 2025 Da Yamma.  Tantirin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya tsallake rijiya da baya bayan mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Sadiku sun yi masa kwanton ɓauna. Dogo Gide ya bayyana cewa ya yi nasara kan ƴan ta'addan inda ya kashe aƙalla guda 20 daga cikinsu tare da ƙwato makamai Dangantaka ɗai ta yi tsami ne tsakanin Dogo Gide da ƴan Boko Haram tun bayan da aka kashe masa ɗan uwansa a shekarar 2023. Jihar Zamfara - Hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya gwabza faɗa da mayaƙan Boko Haram.  Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.  

Yanzu-Ynazu: Donald Trump Na Shirin Ganawa Da Putin

Image
Ina Shirye-Shiryen Ganawa Da Putin-Trump. Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ana shirya yadda zai gana da shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin. Sai dai Mista Trump bai bayyana lokacin da za a yi ganawar ba Yayin da yake jawabi a jihar Florida, shugaban Amurkan mai jiran gado ya ce "Putin na so mu gana, kuma muna shirya yin hakan." Kamfanin dillancin labarai na Rasha, Tass ya ambato kakakin gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov na cewa, har yanzu Amurka ba ta gabatar da buƙatar ganawar a hukumance ba. Trump ya alƙwarta tattaunawa da Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da zarar an rantsar da shi ranar 20 ga watan Janairu, sannan ya bayyana shakku kan tallafin soji da Amurka ke bai wa Ukraine. "Putin na son ganawarmu, kuma ya bayyana ƙarara cewa ya kamata mu kawo ƙarshen wanann yaƙi, wanda ke zubar da jinin al'umma,'' in ji shi. Mista Trump ya naɗa Keith Kellogg, tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, kuma tsohon babban janar a rundunar sojin ƙasa...

Inalillahi!!! 'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro A Katsina

Image
' Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami'an Sa-kai 15 A Katsina. Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da kai wani hari kan wasu jami’an ƙungiyar tsaro ta Community Watch Corps a jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25. Lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an tsaron na Community Watch Corps, suka yi zango a garin Ɓaure na jihar ta Katsina, bayan ziyarar ta’aziyar ɗaya daga cikin abokin aikinsu da ya mutu sakamakon harin ’yanbindigar. Ɗaya daga cikin waɗanda suka shida lamarin ya shaida wa BBC cewa kwantan ɓunar-da ‘yanbindigar suka yi wa jami'an ya janyo mutuwar fiye jami'an na Community Watch Corps 10. ‘’Bayan sun tsaya ne, sai kwatsam ‘yanbindigar suka buɗe musu wuta, kuma sun kashe aƙalla mutum 15’’, in ji shi. Ya kuma ce bayan kashe mutanen ‘yanbidigar sun hana a ɗauki gawarwakinsu har sai ranar Alhamis da safe. Bayan kashe jami’an tsaron na ‘Community Watch Corps’, mutanen gari sun fantsama kasancewar ranar kasuwar gari ne, lamarin da ya sa aka kas...

Yanzu-Ynazu: An Kuɓutar Da Mutanan Da Akayi Garkuwa Dasu

Image
' Ƴan Sa Kai Sun Kuɓutar Da Mutum 8 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Pakistan. Ƴan sa kai a Pakistan sun kuɓutar da wasu ma'aikatan gwamnati 8 da aka yi garkuwa da su a kusa da wurin hakar ma'adinai da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Laraba. Har yanzu ana tsare da wasu da dama a wurare daban-daban na yankin. Rahotanni sun bayyana cewa an jikkata uku daga cikin mazan da aka kuɓutar lokacin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da masu garkuwa da mutanen. Hukumomi na cewa mayaƙan Taliban na Pakistan ne suka yi garkuwa da mutanen a yankin Lakki Marwat da ke gundumar Khyber Pakh-tun-khwa.

Da Dumi-Dumi: Jabun Kaya Sun Mamaye Kasuwannin Nigeria

Image
Jabun Kayayyaki Sun Mamaye Kasuwannin Nijeriya. Ba karamar damuwa ce, musamman ma ga masu kishin Nijeriya,idan aka yi la’akari da sanarwar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi na cewar, ta lalata jabun Magununa da kudinsu ya kai sama da Naira biliyan 120, a cikin watannin shida da suka gabata kacal. Wannan adadin, ya kai na yawan jabun magungunan da Hukumar ta kwace ne daga watannin Oktoba zuwa Disamba na 2024 Adadin, ya jefa matukar fargaba a zukatan al’ummar kasa da ke yin amfani da magungunan wajen nemawa kansu lafiya, musamman ma irin wannan dimbin magungunan na jabun da ake shigowa da su cikin Nijeriya, aka kuma wucewa da su, kai tsaye, zuwa kasuwannin kasar domin sayarwa jama’a.

Alhamdulillah! An Samu Zaman Lafiya Sosai A Kasar Cahdi

Image
Ƙura Ta Lafa A Chadi Bayan Kai Hari Fadar Shugaban Ƙasar. Ƙura ta fara lafawa a N'Djamena, babban birnin ƙasar Chadi, bayan da jami'an tsaro suka daƙile wani hari a fadar gwanatin ƙasar cikin daren da ya gabata. Kakakin gwamnatin ƙasar, Abderaman Koulamallah ya ce maharan na ɗauke da ƙananan makamai. Mista Koulamallah ya ce sojojin ƙasar sun kashe mutum 18 daga cikin maharan tare da kama shida dada cikinsu, yayin da soja guda ya rasa ransa. Abderaman Koulamallah ya ce babban mai shigar da ƙara na ƙasar zai bayar da cikakken bayani kan maharan, amma ya ce ba ya tunanin harin na ta'addanci ne kamar yadda aka yi hasashe tun da farko. Tuni aka tsaurara matakan tsaro a harabar fadar gwamnatin ƙasar.

Mummunan Gobaran Takori Dubban Mutane A California.

Image
Gagarumar Gobara Ta ko ri Dubban Mutane A California. Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta ƙone gidaje ƙurmus a yankuna da dama yayin da take ƙara matsowa zuwa birnin. Mutane sun riƙa ficewa daga motoci suna arcewa a guje domin tsira da rayukansu, wasu sun bayyana lamarin a matsayin tamkar a fim. A cikin sa'o'i kaɗan, iska mai ƙarfin gaske ta ruruta wutar dajin zuwa yankuna da dama na jihar California. Aƙalla mutum 30,000 ne aka bai wa umurnin ficewa daga yankin yayin da gobarar ke bunƙasa, daga fili mai girman eka 10 zuwa 3,000. Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya ce ƴan kwana-kwana sun riƙa umartar mutane su fice daga motocinsu domin tsira daga wutar. Jerin gwanon motoci suna tserewa daga yankin a baya can kuma hayaƙi ya turnuƙe.

Turkashi! An Maka El-Rufai Kotu Kan Zargin lmundahana

Image
ICPC Ta Maka El-Rufai A Kotu Kan Zargin Almundahana. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon kwamishinansa, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi. Jami'in shari'a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka El-Rufai da Bashir Saidu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa. A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohon gwamnan ta almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.

Inalillahi!!! Anci Zarfin Marainiyar Yarinya Abun Tausayi

Image
An Ci Zarafin Wannan Marainiya 'Yar Asalin Jigawa . An yi mata fyaɗe, an tozarta ta, har cokali ake saka mata a gabanta kamar yadda ta faɗa. Yanzu ance gabanta da bayanta sun haɗe. Innalillahi wa inna ilaihi raajiun! Gwamnati da yan sandan Jigawa ba su ga zama ba har sai an yiwa wannan marainiya adalci. Wallahi Tallahi duk mai nauyi akan wannan case idan bai sauke ba, Wallahi nayi imanin ba zai ga dai-dai ba.

Da Dumi-Dumi: An Fara Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai A Borno

Image
An Fara Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai Kan Sojoji  A Borno. Rundunar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan harin da ƴan Boko Haram suka kai wa sojojin ƙasar a sansaninsu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar. Rahotanni sun ce harin na Boko Haram ya yi ajalin aƙalla sojojin Najeriya shida a sansanin sojojin da ke Damboa a ranar Lahadi, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito, inda ta ce tsagin Boko Haram na ISAWP ne suka kai harin. Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da harin, amma bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ba. Sai dai ya ƙara da ecwa, "mun fara bincike kan lamarin. Za mu fitar da sanarwa game da harin nan kusa," kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Wata Sabuwa: Magoya Bayan Peter Obi Sunyi Allah Wadai Da Barazanan Rayuwarsa.

Image
Magoya Bayan Peter Obi Sun Yi  Allah-wadai Da Barazana Ga Rayuwarsa. Magoya bayan tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya, Peter Obi, wato Obidient sun yi Allah-wadai da barazanar da ya ce ana yi wa rayuwarsa. A wata sanarwa da Yunusa Tanko ya fitar a madadinsu, ya ce suna takaici kan jawabin Felix Morka wanda sakataren watsa labaran APC ne na ƙasa ya yi a tashar Arise. Sanarwar ta ce, "maganarsa cewa Peter Obi ya tsallake iyaka barazana ce ga rayuwarsa, kuma barazana ce ga zaman lafiyar Najeriya. "Wannan na nuna yadda Najeriya take ƙara faɗawa cikin mulkin kama-karya a wannan gwamnatin, domin a ce irin wannan jawabin na fitowa daga bakin kakakin jam'iyya mai mulki bai da ce ba, kuma tamkar kira ne ga tayar da zaune tsaye. Sanarwar ta kuma yi tambayar "wane ne ya shata layin, kuma wane layin ne Obi ya tsallaka?" sannan suka yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa.

Yanzu-Ynazu: Girgizar ƙasa Tayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Sama Da 75 A China

Image
Aƙalla Mutum 95 Sun   R asu A Girgizar ƙasa A China. Bayanan hoto,Aƙalla gidaje 1,000 ne suka ruguje a girgizar ƙasar sannan mutum 95 suka rasu Wata mummunar girgizar ƙasa ta afku a kusa da iyakar Tibet da Nepal. Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da 130 sun jikkata a girgizar, wadda ta afku a ranar Talata. Girgizar ta kuma ƙetara zuwa yankin Nepal da ke ƙasar Indiya, wanda ke maƙwabtaka da Tibet na ƙasar China. Girgizar ƙasar ta lalata gine-gine a birnin Shigatse na Tibet, lamarin da ya sa jama'a su riƙa kwararowa kan tituna domin tsira.   Tuni sojojin ƙasar suka fara aikin ceto, inda suka aika jirage marasa matuƙa zuwa wani yanki mai nisa a kusa da tsaunin Everest

Turkashi: "Rayuwata Na Cikin Hadari Da Barazana" prter Obi.

Image
"Ana Barazana Ga Rayuwata" Peter Obi. Ɗantakarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar gwmnatin Shugaban Ƙasa Tinubu da ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara. A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya. A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce, "shin na wuce iyaka? na yi wannan tambayar ce saboda ana yi wa rayuwata da ta iyalina barazana saboda jawabin da na yi na sabuwar shekara.  Bayan barazanar kuma, wani mai suna Mr Felix Morka ya zarge ni da wuce iyaka, sannan ya yi barazanar zan ɗanɗana kuɗata," in ji shi. Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna masa, inda ya ƙara da cewa, "amma ba zan daina faɗin gaskiya ba, musamman a wannan lokacin da ƙasarmu ke ƙara shida cikin ruɗu.

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Bauchi Ya Kori Kwamishinoni Biyar

Image
Gwamna Bala Ya Fatattaki Kwamishinoni 5 A Gwamnatinsa, Ya Ba Daa Sunayen Sababbi 8.    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa domin inganta shugabanci da tabbatar da nagartaccen aiki ga al'umma Sanarwa ta bayyana cewa an tsige kwamishinonin ne domin kawo sababbin dabaru da kuzari don magance kalubalen da ke gaban gwamnati tare da kyautata ayyuka.  An Kuma tura sunayen mutane takwas don tantancewa a matsayin sababbin kwamishinoni, yayin da gwamnan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta rayuwar al'ummar jihar. Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da sauye-sauye a gwamnatinsa tare da tsige wasu kwamishinoni guda biyar. Gwamnan ya ce ya dauki wannan mataki ne domin inganta shugabanci a gwamnatinsa da tabbatar da nagartaccen aiki.  Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a shafin Facebook.

Inalillahi! Allah Yayi Wa Babban Malamin Musulunci Rasuwa.

Image
Babban Malamin Musulunci Ya Rasu  A Gombe, Farfesa Pantami Ya Magantu. Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, Sarkin Malaman Funakaye.  Malam Adamu Abubakar Bajoga Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025 wanda aka gudanar da jana'izarsa a safiyar Litinin 6 ga watan Janairun 2025 Bajoga, Gombe - An shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe, Malam Adamu Abubakar Bajoga.  Marigayin ya rasa ransa ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025 inda aka yi jana'izarsa a safiyar ranar Litinin a garin Bajoga da ke jihar Gombe.  Gombe: An yi jana'izar babban malamin Musulunci Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya mika sakon ta'aziyyarsa a gajeren rubutu da ya yi a sha

Da Dumi_Dumi: 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji Da Dama A Borno.

Image
Iswap Ta kashe Sojojin Najeriya Shida A Jihar Borno, Inji Rahoton AFP Mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State sun kashe sojojin Najeriya shida yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP. AFP ya ambato jami'an sojin Najeriya biyu na cewa maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (Iswap) sun far wa sansanin da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ranar Lahadi da tsakar dare. Rahotonni sun ce sun cinna wa sansanin wuta tare da ababen hawan da ke cikinsa. "An kashe mana sojoji shida a harin na Iswap da suka kai sansanin bayan zazzafar musayar wuta," kamar yadda ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa wa AFP. Ɗaya jami'in ya ce jirgin sojin sama da aka aika daga binrin Maiduguri, mai nisan kilomita 100, shi ne ya kori maharan. "Hare-hare ta sama ya kashe 'yanbindigar da yawa, ya lalata motoci da makamansu," in ji majiyar ba tare da bayar da yawan adadi ba

Turkashi! Kotu Taba Da Damar Kama Tsohuwar Shugaban Bangladesh

Image
Kotu Ta Bayar Da Sammacin Kama Tsohuwar Shugaban Bangladesh .   Wata kotu a ƙasar Bangladesh ta bayar da sammacin kama tsohuwar Shugabar Ƙasar, Sheikh Hasina, wadda ta samu mafaka a ƙasar India. Masu gabatar da ƙara sun bayan ita, an kuma bayar da sammacin kama wasu mutanen guda 10, ciki har da tsohon mai ba shugaban ƙasar shawara kan tsaro. Ms Hasina ta tsere ne zuwa India bayan zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar a watan Agustan. Aƙalla mutum 500 ne ake zargin cewa jami'an tsaron ƙasar sun sace a shekara 15 da ta yi tana mulkin ƙasar. A watan Disambann bara ne ƙasar ta buƙaci India ta mayar da tshohuwar firaiministan domin ta fuskanci shari'ar zargin da ake mata

Yanzu_Yanzu: An Harbe Ƴan Israela A Gaɓar Yamma.

Image
An Harbe Ƴan Isra'ila Uku A Ga ɓar  Yamma. An harbe wasu ƴan Isra'ila guda uku a wani hari da aka kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. Mata biyu waɗanda suka kai shekara 60 suna cikin waɗanda aka harbe. Rundunar tsaron Isra'ila ta ce wasu ƴanbindiga ne suka buɗe wuta kan motocin fararen hula guda uku a lokacin da suke wucewa ta wani ƙauyen yankin mutanen Falasɗinu mai suna Al-Funduq wanda ke kusa da garin Yahudawa na Kedumim. Tuni jami'an tsaron Isra'ila suka kafa shingayen bincike a yankin da zimmar kama waɗanda suka kai harin.

Wata Sabuwa: Za Akarɓe Mulki Ahannu APC.

Image
Za Mu karɓe Mulki A Hannun APC A 2027 – PDP. Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta ce za su samu ƙarin gwamnoni a zaɓen 2027, ƙari a kan guda 12 da take da su a yanzu, sannan ta karɓe mulkin ƙasar. Jagororin jam'iyyar ne suka bayyaka haka a lokacin da suka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Ma'ajin jam'iyyar, Alhaji Ahmed Yayare ne bayyana hakan a madadin jam'iyyar, inda ya ce yanayin yadda ƙasar ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziki ne ya sa PDP za ta samu sauƙin samun nasara a 2027. Ya ƙara da cewa, "babu abin da zai hana PDP karɓe mulkin ƙasar. Yanzu APC ba ta abin da za ta yi kamfe da shi saboda yunwa da talauci ya yi a ƙasar. Idan suka fita kamfe sai an jefe su."

Albishirinku! Kayattacan Shirin JAMILUN JIDDA Zai Fara Zuwa Maku Ranar Asabar.

Image
Albishirinku!!! Ina Mai Farin Cikin Sanar Da  ku Cewa Kasaitaccen Shirin JAMILUN JIDDA Zai Fara Zuwa Maku Ranar Asabar 11 GA Watan Junairu 2025 Da Misalin Karfe 9:00pm Na Dare Akan Talabijin. #AREWA24 #TAKUCE

Innalillahi! Wasu Matasa Sun Kona Wani Mutum Har Lahira

Image
Zargin Maita': Wasu Fusatattun Matasa Sun Bankawa Ɗan Najeriya Wuta Har Lahira .   Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama mutane 17 da ake zargi da kashe wani mutumi a jihar Ebonyi, bisa zargin yana maita An zargi Uromchi Okorocha, da zama silar mutuwar wasu mutane ta hanyar lashe kurwarsu. Alamarin da ya jawo aka kona shi Sufeto janar na ‘yan sanda ya yi Allah wadai da masu daukar doka a hannu, yana kira ga al’umma su rika kai rahoto ga hukumomi  Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas ta kama mutane 17 da ake zargi da kona wani mutum bisa zargin maita. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce lamarin ya faru a ranar 3 ga Janairu.